Kannywood

Saura ƙiris na yi wuf da wani, inji Hauwa Waraka

fitacciyar jaruma Hauwa Abubakar (Waraka) ta kori ji-ta-ji-tar da wasu ke yaɗawa cewa ta ƙi yin aure, inda ta bayyana cewa saura kaɗan ta yi “wuf” da wani.
Kamar yadda fimmagazine na ruwaito.Waraka, wadda tauraron ta ke haskawa a wannan zamani kuma ta na ɗaya daga cikin matan Kannywood sanannu, ta bayyana hakan ne a zantawar ta da mujallar Fim.
Furucin jarumar na zuwa ne a daidai lokacin da matan Kannywood ke ƙoƙarin curewa wuri ɗaya domin samar wa kan su mafita daga abin da su ka kira barin su a baya da mazan harkar su ka yi a al’amura da dama.
Don haka ta yi cikakken bayani kan taron da Ƙungiyar Matan Kannywoood (Kannywood Women Association of Nigeria, K-WAN) ta shirya a Kano a makon jiya domin sada zumunta da inganta haɗin kan matan industiri.
Waraka ta bayyana taron a matsayin wata alama ta samun nasara a gwagwarmayar da matan ke yi domin samun ‘yanci.
Bugu da ƙari, ta bayyana irin farin cikin ta da ta halarci taron na K-WAN, ta ce ta daɗe ba ta ga irin wannan taro a masana’antar finafinan ba.
A cewar ta, “Irin farin cikin da na ke tare da shi a yanzu ba ya misaltuwa saboda na ji daɗi sosai, don na daɗe ban je wani taro irin na Kannywood haka ba.
“Gaskiya zan iya cewa na fi shekara ban je wani taro ba sai wannan. Na ji daɗi saboda mun haɗu da mutane da dama, har da waɗanda ma tun kafin ka san za ka shigo harkar fim ɗin su ke fim, da waɗanda ma sai bayan ka shigo su ka shigo kuma an daɗe ba a haɗu ba, ga shi duk an harhaɗu an sada zumunci an gaisa, kowa ya ga kowa.
“Kuma taro ne na mata zalla na Kannywood, da tsofaffi da mawaƙa da jarumai da furodusoshi da daraktoci mata da sauran su.”
A kan batun haɗin kan matan masana’antar da K-WAN ke ƙoƙarin wanzarwa, Hauwa Waraka ta ce, “Ina ganin wannan ƙungiya ba ƙaramin karɓuwa ta yi ba a industiri saboda da man ƙungiyar ta matan Kannywood ce zalla, ba wai har da matan waje ba, iya mu-i-mu ne.”
Hauwa Waraka ta na yi wa jaruma Teema Makamashi liƙi a wajen taron K-WAN da aka yi a Kano a makon jiya
Ta yi nuni da cewa, “A gaskiya an daɗe ana kafa ƙungiyoyi da yawa irin na mata haka na Kannywood, amma ba a taɓa samun wadda ta daɗe kowa ya ke bada gudunmawa ɗari bisa ɗari irin wannan ƙungiya ba. Na daɗe ban ga an yi ƙungiyar da ta haɗa jarumai an yi wani taro na musamman don matan Kannywood ba sai a gun K-WAN.”
Waraka ta bayyana ƙungiyar a matsayin wata katanga da ya kamata matan na Kannywood su jingina da ita domin samar musu da ‘yanci.
Ta ce: “Wannan ƙungiya za ta dawo mana da martabar mu tare da ƙwato mana haƙƙin mu da mu ke gani ana take mana, saboda ana yin abubuwa da dama a Kannywood ana barin mata da dama a baya.”
Da ta ke bayani kan musabbabin kafa ƙungiyar, jarumar ta shaida wa mujallar Fim cewa: “Ga abubuwan cigaba da dama amma ba a sa mata sai dai maza kawai don ba za a taɓa ji an ce an bai wa mace gudunmawa da za ta kai ga gaci ko an kai ga abin da ake so ba.
“Wannan dalilin ne (ya sanya) mu ka tashi tsaye tunda ana haɗa ƙungiyoyi na maza su na haɗa kan su don yin abubuwa na cigaba, sai mu ma mu ka ce me zai hana mu yi wata ƙungiya tamu ta musamman ta matan Kannywood wadda za mu dinga taimaka wa kan mu, mu kuma kai kan mu ga gaci har mu samu cigaba da ba ma tunani a ciki, duk da dai yanzu jaririya ce ana rainon ta sai a hankali.”
To sai dai da ta ke wa wakilin mu ƙarin haske kan raɗe-raɗin cewar ta kusa yin aure, sai ta yi dariya ta ce, “Gaskiya kam, to ga shi nan dai in ta kama na yi wuf da wani to zan yi; in kuma ni aka yi wuf da ni, to ba mamaki. Za a yi wuf da ni ɗin nan ba da jimawa ba.”
A ƙarshe, Hauwa Waraka ta yi godiya ga masoyan ta saboda irin goyon bayan da su ke ba ta a ko da yaushe.
Ta ce, “Ina gode wa masoya na a kan irin gudunmawar da su ke ba ni da kuma irin ƙaunar da su ke nuna min, da daɗi ba daɗi su na tare da ni.
“Duk wani motsi na da wani abubuwa na za ka ga in ya tashi in na farin ciki ne su na taya ni farin ciki, haka kuma in na baƙin ciki ne su na taya ni baƙin ciki.
“Wallahi ba abin da zan ce da masoya na sai godiya, saboda in dai a industiri ne ba ka da masoya sai dai a ce ma kawai ka yi haƙuri. Don haka ina gode wa masoya na, ina gode musu godiya mara adadi, mara misaltuwa.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button