Labarai

Gwamnatinmu Ta Biya Dukkan Bashin Da Ake Bin Nijeriya Daga 1999 Zuwa 2007- Martanin Atiku Ga Buhari

A ranar murna samun iyan cin kai Shugaban kasa Muhammad buhari yayi jawabi wanda  daga cikin jawabinsa yace duk wani irin da na Nigeria take cikin ta samu asali ne tun 1999-2015.

Shine Atiku Abubakar yayi Martani akan cewa duk wani bashi da ake bin na nigeria an biyashi shi, shafin rariya sun ruwaito cewa:

 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya mayar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da martani kan jawabinsa na bikin cika shekaru 60 da samun ƴancin Nijeriya.

A cikin jawabin da shugaba Buhari ya gabatar, ya zargi shugabannin da ya gada daga 1999 zuwa 2015 da ƙoƙarin durƙusar da Nijeriya, inda ya ce ba su da bakin sukar gwamnatinsa.

Amma a martaninsa, Atiku babban abokin hamayyar Buhari a zaɓen 2019, ya ce tsakanin 1999 zuwa 2007, ba a bin Nijeriya bashi domin sun biya bashin da aka bi Nijeriya.

Atiku ya kuma kara da cewa yana alfahari da ayyukan da shi da shugaba Obasanjo suka yi wa kasarsu Nijeriya.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA