Labarai

Ya kamata Majalisa ta tsige Shugaba Buhari daga Mulki ~A’isha Yusuf

Advertisment

Jagorar gangamin neman a saki ‘yan matan Chibok, A’isha Yusuf ta bayyana cewa ya kamata majalisa ta tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga mulki.

A’isha ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumunta inda take maida martani kan kiran da majalisa ta yi na cewa shugaba Buhari ya cire shuwagabannin tsaro.

Tace ‘yan Majalisar sun yi iya nasu akan cire shuwagabannin tsaron tunda sun gayawa shugaba Buhari, yanzu nashi ya rage a matsayinshi na kwamandan Askarawan Najeriya.

Tace a bayyane yake shugaba Buhari ya gaza kuma bai kamata a tsaya wani boye-boye ba, tace Najeriya ba zata iya jira a ci gaba da samun irin wannan matsalar tsaro har nan da shekaru 3 ba, dan haka kawai majalisar ta tsige shugaban kasar.hutudole ya ruwaito wannan labari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button