Suleman Panshekara Da Masoyiyarsa ‘Yar Amurka Sun Je Yawon Bude Ido A Wani Kauyen Kano (Kalli Hotuna)
Daga Nura Siniya
Suleiman Panshekara matashi mai kimanin shekaru 23 dan asalin jihar Kano, kenan yayin da ya fita yawon shakatawa da bude ido a garin ‘Yan Danko dake jahar Kano, tare da masoyiyar sa, abin kaunar sa, kuma kwankwalaton zuciyar sa kyakkyawar baturiyar nan mai suna Jaenine samchez mai kimanin shekaru 46 da haihuwa wacce tsuntsun soyayya ya dauko zuwa jahar kano gurin masoyin nata suleiman da nufin cikar burin ta na ganin cewa ta aure shi, wanda ta zo tun daga birnin Califonia dake kasar Amurika.
Suleiman ya zazzagaya da masoyiyar tasa (Jaenine) ta ganema idanuwan ta wasu daga cikin al’adun gargajiya irin na Hausa/Fulani wanda ya shigar da ita a cikin kwale-kwale suka ketare ruwa gulbi zuwa garin Dan danko, ya siya Mata karas da rake ta sha ta koshi har suka yi guzuri da shi zuwa gida.
Suleiman tuni suka dade suna tsunkar furannin soyayya shida Baturiyar ‘yar kimanin shekaru 46 da haihuwa wanda tun kafin zuwan ta Nijeriya sun dade suna yi wa junan su wata irin makauniyar soyayya tun a kafar sadarwa ta Instagram inda ta nan ne suka hadu da wanda yanzu haka sun cimma matsaya game da auren su.
Baturiyar dai (Jaenine Sanchez) ta yi nisa cikin kogin son matashi Suleiman, wanda hakan ya sa ta amince da dukkan sharuddan da mahaifan shi suka sanya mata wanda lamarin ya je har ga hukumar Hisba ta jihar Kano.
Baturiyar dai a cikin sharuddan da aka kafa Mata na auren Suleman ta amince za ta bar shi ya karasa karatun shi da digiri a can birnin Califonia da ba shi cikakkiyar kulawa ta musamman mai cike da annuri irin ta ma’auranta zamani tare barin shi yana ziyartar gida Nijeriya, domin duba iyayen sa da kuma ‘yan uwa da abokan arziki.
A wata hira da BBC ta yi da matashin Suleiman a lokacin da suka ziyarci gidan zoo na Kano, domin shakatawa da Baturiyar ya bayyana cewa yanzu yake soyayya kuma ya san dadin so har yake cewa ba zai kara yin soyayya da wata yarinya ‘yar Nijeriya saboda matan Nijeriya ba su iya soyayya ba.
Yanzu Haka dai masoyan sun saka ranar auren su wanda zai kasance 28-ga watan March, 2020, zarar an daura Suleman da amaryar as Jaenina Sanchez za su shilla zuwa birnin Calfonia na kasar Amurka.
Allah (SWT) ya sa sanadiyar Suleiman wannan Baturiya ta karbi kalmar shahada ta dawo cikin addinin musulunci.