Yan Bindiga Talatin Sun Mutu A Yayin Wani Rikici Tsakanin Su Wurin Raba Dabbobi Da Suka Sato
Wani kazamin rikici da ya barke a tsakanin yan bindiga a Jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 30 daga cikin su, wasu kuma suka samu munanan raunuka.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kawaye dake Karamar hukumar mulkin Anka a Jihar ta Zamfara kamar yadda wani mazaunin wurin da ya nemi a sakaya sunan shi ya ce, fadan ya tashi ne a lokacin da yan bindigar ke rabon shanun da suka sato,kamar yadda jaridar voahausa na ruwaito.
“Barayi ne sun koro shanu daga Arewa, to, wurin rabon shanun sai aka baiwa wasu yan kadan wasu aka basu masu yawa, shine sai fada ya barke a tsakanin su, suka dinga musayar wuta, an kashe barawo zai kai talatin (30), yanzu haka akwai wasu da zasu kai ashirin suna jinya,” in ji shi
Har ila yau ya ce an yi fadan ne a Dajin Kawaye, tsakanin yaran wasu manyan yan bindigar wato yaran Kachalla Halilu da yaran Bello Kaura, ya ce sun ji lokacin da ake musayar wutar kuma sun gano adadin wadanda aka kashen ne ta hanyar labarin da yaran yan bindigar ke yi har ya iso a kunnuwan su.
Shi ma wani mazaunin wani kauyen da ke makwaftaka da wajen da lamarin ya faru, ya ce rikicin har ya shafi wasu masu wankin zinari a dajin wadanda har sashen yan bindigar dake yakar junan su ya riske su.
“Sun sato shanu da rakumma sun fi 1000 daga yankin Sakkwato, wurin rabon su ne suka samu rashin fahimtar juna har fada ya faru a tsakanin su, kuma sun yi barna sosai don sun harbi mutane da dama, don ina ganin yanzu akwai kusan mutun 17 kwance a asibitin Nasarawa,” a cewar wani mazaunin yankin.
To Sai dai duk kokarin da wakilin Sashen Hausa ya yi don jin ta bakin rundunar yan sanda dake jihar abun ya ci tura, domin duka kiraye kirayen waya da gajerun sakonni da ya aikawa kwamishin yan sandan jihar CP Shehu Muhammad Dalijan bai samu amsar sakonnin ba.
Saurari cikakken rahoto a nan.