Tsadar Kayan Abincin : Koke Zuwa Ga Shugaba Buhari ~ Daga Datti assalafy
Muna yiwa Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari fatan alheri da samun nasara a shugabancinka
Bayan haka wannan sako koke ne da korafi zuwa ga Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari, hakika kayan abinci yayi tsada da tsananin da ba mu taba gani ko jin duriyarsa ba a tarihin Nigeria
Babu abinda baiyi tsada ba yanzu a Nigeria, komai ya kara kudi, mutanen da suke iya cin abinci sau uku a rana sun dawo suna ci sau biyu, masu ci sau biyu sun dawo sau daya saboda yadda kayan abinci yayi tsada
Duk wani abinda gwamnati zatayi na gina kasa shirme ne da kuma aikin banza idan har ba’a saukakawa talaka ya samu abinci da zaici ya rayu ba, abu biyu talaka yake bukata, tsaro da kuma abinci, duk wani abu bayan wannan shirme ne da aikin banza da shiririta
Babu amfanin rufe bodar Nigeria a yanzu kam, ance an dauki mataki a kan rufe boda don a dakile safarar miyagun makamai amma hakan bai amfanar da komai ba, miyagun makamai suna shigowa fiye da kafin ma a rufe bodar
Ance an rufe boda an haramta shigo da shinkafar Kasar waje domin mu koma ga noma ya zamto muna noma abincin da zamu iya ci, an koma ga noma, ana noma sosai, wannan ma bai haifar da komai ba, sai tsananin tsadar rayuwa
Ka haramta shigo da shinkafa ‘yar kasar waje, amma na tabbata gidanka shinkafar kasar waje a ke ci, hakanan manyan mukarrabanka, wannan ba adalci bane, idan tsarin mulki yace shugaban kasa da mukarrabansa akwai kaso na kudi daga asusun gwamnati da za’a dinga ciyar da su, to su kuma talakawa fa?, da kana sayen shinkafa da kudin albashinka da ka fi fahimtar koken talakawa
Shugaba Buhari kaji tsoron Allah, indai bude boda shine abinda zai kawo sauki ga kayan abinci to don girman Allah ka bude, ka sani yunwa tana kashe takalawanka, Allah Zai kamaka da laifi babu shakka
Shugaba Buhari kowa haushinka yake ji a yanzu saboda wannan tsada na abinci, martabanka, soyayyarka da kuma darajarka ta ragu a gurin talakawa, ka samar da mafita, kayi abu mai kyau da tarihi zai tuna da kai
Muna rokon Allah Ya taimaki shugaba Buhari, Ya bashi ikon samar da saukin rayuwa a Nigeria Amin