Labarai

Talakawa suna mutuwa da yunwa a gwamnatin mu ta Apc – Dan balki kwamanda

Advertisment

Shahararren dan gwagwarmaya nan mai suna Abdulmajeed almustapha wanda anka fi sani da dan balki kwamanda yayi tsokaci sosai akan tsada rayuwa da mutane sune ciki.

Dan balki kwamanda a cikin wani faifan bidiyo da ke yawa a facebook nan ne yake bayyana irin halin da talakan arewacin najeriya yake cikin inda yake cewa.

Talakawa suna mutuwa da yunwa a gwamnatin mu ta Apc - Dan balki kwamanda
Talakawa suna mutuwa da yunwa a gwamnatin mu ta Apc – Dan balki kwamanda

Ga abinda yake cewa:

“Amma inaso in fadama mai girma sanata bola Ahmad tinubu da mai girma sanata mataimakin sa kashim shettima , mai girma kashim shettima wallahi hakkin mu na a kanka na arewa dole ka tashi kayi kokarin da zaka iya akwai abinda bazaka iya ba mun sani,amma mutanenka suna cikin wani hali na rantse maka da Allah yanzu, na rantse maka da Allah sau ukku mutane mutuwa suke da yunwa a arewa billazil azimu a karkashin gwamnatin mu , mutuwa suke mutuwa saboda yunwa billazil azimu a kauye da birni saboda yunwa.

Saboda ahmad bola mai girma shugaban kasa da kashim shettima mu dauki matakin farfado da mutane yunwa tana kashe talakawa a arewa sa nan ga ba zama lafiya ga yunwa ga sauro ga masifa ga minene sunyiwa talakawa yawa kuma su suka zabe mu dan haka muna gayamuku gaskiya, bama son talakawa su bijirewa jam’iyar mu ta Apc.

Kuyi duk abinda zakuyi talakawan arewa yunwa tana kashe talakawan arewa kuma idan kaje magani a asibiti babu ina tabbatarwa da shugabannin mu idan kunne yaji jiki ya tsira , bama so talakawa su bijire muku saboda idan talakawa sunka bijire muku baku da ma’aikatan da zasu iya kula da su.

Talakawa suna mutuwa a arewa, talakawa suna cikin masifa arewa ,jam’iya ta APC dole ki dau mataki da talakawan da suka zabe mu suka yadda da muslim muslim ticket, idan baso kuke nan gaba ba su rinka cewa ba ruwansu da Muslim muslim ticket, ku barmu da wahala tunda mu muke talla ku kuna gidan gwamnati ko kuma kuna cikin tsaro, mu kuma mushiga nan mushiga nan mushiga kwazazzabo mu shiga rafi dan mu samu muku magoya baya saboda mu ‘ya’yan talakawa ne suk yarda da mu domin baza mu cutar da su ba, bazamu yaudare su ba.

Amma ina tabbatarwa da shuwagani yunwa tana kashe talakawa shine sakon da nake so gayawa al’umma inji shi.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button