‘Yar Kannywood zan Aura ! Maishadda Ya Bayyani Jarumar Da Zai Aura
Abubakar Bashir Maishadda wanda ya ke yi wa kan sa lakabi da ‘King of Kannywood Box office’ matashi ne da ya yi fice a masana’antar fim ta Kannywood kuma a cikin ‘yan kwanakin nan ya na daya daga cikin masu jan ragamar masana’antar wajen shirya fina-finai a kai a kai, musamman a lokacin da masana’antar ta yi sanyi sakamakon rashin samun kudin shiga da masu shirya fim ke korafi a kai.
Sai dai Maishadda ya bayyanawa duniya cewa matar da zai aura ta na cikin masana’antar Kannywood, kuma nan ba da dadewa ba za su yi aure. Ya bayyana sunan Hassana Mohd a matsayin masoyiyar sa a wata hira da mu ka yi da shi kai tsaye a Instagram live chat a ranar Lahadin da ta gabata.
Tambayar da mai jagorancin shirin Jamilu Abdussalam ya yi masa a kan menene gaskiyar soyayyar sa da Hassana Mohd kamar yadda a ke ganin sa ya na yawan sa hotunan ta a shafin sa na soshiyal midiya da kuma yawan sanya ta a fina-finan sa. sai matashin ya ce “Kwarai Hassana Mohd budurwa ta ce kuma ita ce wacce zan aura nan ba da dadewa insha Allahu”. A cewar Maishadda.
Wannan jawabi dai na Maishadda ya biyo baya ne sakamakon cewa da masu bibiyan shirin su ka yi wajen sai ya furta hakan, a cikin wadan da su ka tisa shi a gaba cikin raha har da shahararriyar Jaruma kuma mai shirya fim a masana’antar, Rukayya Dawayya.
#northflix