Duk wanda ya kira ni kan ci gaban Kannywood zan je – Naburaska


Fitaccen Jarumin masana’antar shirya fina-finan hausa ta Kannaywood Mustapha Badamasi Naburaska ya ce, duk dan siyasar da ya kira su domin tattaunawa kan ci gaban sana’ar su kai tsaye za su je wurin sa babu duba jam’iyyar da ya fito.
Kamar yadda DALAFIM na ruwaito cewa mustapha Naburaska, ya bayyana hakan ne a cikin wani shiri na musamman da ya gudana a gidan rediyon Dala a ranar Laraba.
Ya ce, “Duk da cewar ina jam’iyyar PDP tsagin Kwankwasiyya, idan Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kira ni domin baiwa Kannywood ci gaba kai tsaye zai je wurin sa, amma hakan ba ya na nufin na bar jam’iyyar da nake so ba ne”.
Ya kuma ce, “Gani na tare da gwamnan jihar Sakoto Aminu Waziri ba zai taba min siyasa ta da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ba”. Inji Naburaska.
Naburaska ya kuma kara da cewar, shugabannin hukumar tace fina-finan hausa na lokacin mulkin Ganduje sun gaza wajen ci gaban sana’ar, a daidai wannan lokacin da kasuwancin ta ya durkushe.

