Addini

Maulidi Bidi’a Ne Inji Shehu Uthman Dan Fodiyo – Dr. Jalo Jalingo

Advertisment

 Dr. Ibrahim Jalo Jalingo yace: Babban Malami kuma Mujaddidin Musulunci Sheikh Uthman Dan Fodiyo ya ce: Maulidi bidi’a ce abar kyama.
 Shehu ya rubuta cikin  littafinsa mai suna: Ihyaa’us Sunnah Wa Iqmaadul Bid’ah shafi na 104 kamar haka:

(( ﻓﺎﻥ ﻗﻠﺖ ﻣﺎ ﺣﻜﻢ ﻣﺎ ﻳﻔﻌﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﺷﻬﺮ ﺭﺑﻴﻊ ﺍﻻﻭﻝ ﻓﻲ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻭ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺍﻟﺴﺎﺑﻊ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﻣﻦ ﺍﺟﺘﻤﺎﻉ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻟﻠﺬﻛﺮ ﻭﺍﻟﻄﻌﺎﻡ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﻌﻤﻠﻮﻧﻪ ﻟﺬﻟﻚ؟ ﻗﻠﺖ : ﺍﻧﻪ ﺑﺪﻋﺔ ﻣﻜﺮﻭﻫﺔ ﺍﻥ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻛﻞ ﻣﻌﺼﻴﺔ . ﻭﻗﻴﻞ : ﺍﻥ ﺍﻟﺼﻮﺍﺏ ﺍﻥ ﻋﻤﻞ ﺍﻟﻤﻮﻟﺪ ﺍﻟﺸﺮﻳﻒ ﺍﻟﻨﺒﻮﻱ ﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺍﻟﺤﺴﻨﺔ ﺍﻟﻤﻨﺪﻭﺑﺔ ﺍﺫﺍ ﺧﻼ ﻋﻦ ﻣﻌﺼﻴﺔ . ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺎ ﻳﻌﺘﺎﺩﻩ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ ﻓﻲ ﺫﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﺧﺘﻼﻁ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻓﻤﻌﺎﺫ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﻳﻘﻮﻝ ﺍﺣﺪ ﺑﺠﻮﺍﺯﻩ )).

Ma’ana: ((Idan ka ce: Mene ne hukuncin abin da mutane suke yi a cikin watan Rabii’ul Awwal a ranar maulidi, ko kuwa a ranar bakwai ga maulidi na taruwar jama’a saboda yin zikiri, da cin abincin da aka yi tanadinsa saboda hakan? Sai in ce: Wannan bidi’ah ce makruuhiyah in yin maulidin ya kubuta daga dukkan sabon Allah.
(A wani kaulin kuma) an ce: Abin da yake daidai shi ne: shirya maulidin Annabi yana daga cikin bidi’o’i masu kyau da a ake so matukar dai ya kubuta daga ko wane sabon Allah.
To amma abin da mutane suka Saba yin shi a maulidi a wannan zamani na cakuda tsakanin maza da mata A’uuzu Billaahi wani ya yadda da halaccinsa)).

A cikin wannan magana ta Shehu Uthman Dan Fodiyo za mu fahimci abubuwa muhimmai kamar haka:-
1. Fatawar Sheikh Uthman Dan Fodiyo ita ce: Bukin Maulidi bidi’ah ce makruhiya, watau bidi’ah abar kyama.
2. Akwai wata magana da ke cewa: Bukin Maulidi bidi’ah ce da ake so, to amma shi Sheikh Uthman Dan Fodiyo yana ganin wannan magana mai rauni ce; wannan shi ne ma ya sa ya hikaito maganar da sigar tamriidhi.

Advertisment

Allah muke roko da ya tausaya wa al’ummarmu Ya cusa musu kyamatar bidi’ah duk yadda Shaidan zai yi  kawata ta cikin zukatansu. Inji Dr. Ibrahim Jalo Jalingo.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button