AddiniLabarai

Gwamnatin Kano Ta Haramtawa Abduljabar wa’azi A duk Fadin Jahar kano

Majalisar zartarwar jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta amince da haramta wa fitaccen malamin addinin Islama na jihar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara yin wa’azi a dukkanin faɗin jihar nan take.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Muhammadu Garba ne ya tabbatar da hakan ga BBC.
Ya ce an tattauna batun yayin zaman majalisar na ranar Laraba bayan wasu rahotanni da ke nuna cewa malamin na yin kalaman da ka iya haifar da fitina a jihar.
”Gwamnati ta tsaya ta yi nazari, kuma ta samu rahotanni daga wurare daban-daban, har akwai rahotanni daga wajen manyan malamai da kuma hukumomin tsaro, dalilin da ya sa jami’an tsaro suka sanya kwamiti na musamman don duba irin waɗannan kamalamai da malamin ke yi” a cewarsa.
Ya ce sakamakon tattaunawa a kan wannan batu da majalisar zartarwar jihar Kanon ta yi ne yasa ta amince da cewa, ba shakka kalaman nasa na iya haifar da tarzoma, don haka ta bada umarnin hana shi yin wa’azi a ko ina a faɗin jihar.
Matakan da aka ɗauka a kan Sheikh Abduljabbar sun haɗar da rufe masallacinsa dake unguwar Filin Mushe, da kuma hana shi yin wa’azi ko huɗuba a ko ina fadin Kano.
Kazalika an shawarce shi ya guji yin kalaman tashin hankali a ko ina ciki har da kafafen sada zumunta da ake yaɗa wa’azinsa, har zuwa lokacin da hukumomi za su kammala bincike.
Gwamnati ta buƙaci kafafen watsa labarai a jihar su kauce wa sanya wa’azinsa, tana mai cewa yin hakan ma na iya haifar da tashin hankali a cewarsa.
Ko da BBC ta tambaye shi ko an zauna da malamin kafin ɗaukar wannan mataki, sai ya ce jami’an tsaro sun zauna da shi, kuma sun lura cewa akwai ƙanshin gaskiya a zargin da ake yi masa.
Kwamishinan yaɗa labaran ya kuma ƙaryata cewa matakin da aka ɗauka na da alaƙa da siyasa, musamman ga masu ganin cewa akwai wata a ƙasa tsakaninsa da kuma gwamnatin jihar Kano.
Bayanan bidiyo,
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Shiekh Abduljabbar Nasiru Kabara
”Wannan magana ce ta zaman lafiya, kuma na san ko su ƴan Kwankwasiyya ba za su so a riƙa yin kalaman da za su janyo tashin hankali ba, sannan ba wani zaɓe ne a gabanmu ba ballantana a yi zargin cewa akwai siyasa, don haka magana ce ta tabbatar da tsaro a jihar Kano,” in ji Muhammadu Garba.
Wata tambaya da BBC ta yi wa kwamishin ita ce ko wannan haramtcin na wani ɗan lokaci ce ko na din-din-din, sai ya ce an kafa kwamiti domin gudanar da bincike, da zarar ya kammala bincikensa za a san matakin da za a ɗauka na karshe.
A baya an samu takun-saka tsakanin malamin da wasu malaman jihar Kano wadanda suke ganin yana yin kalamai da suka saba wa addinin Musulunci, sai dai ya sha musanta wannan zargi inda ya ce galibin abubuwan da yake fada ya samo su ne a littafan Musulunci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button