Uncategorized

AL’AJABI : Karanta Labarin Karen Da Ya Kashe Wani Banasare Saboda Ya Zagi Manzon Allah SAW

Babban malami allama Ibnu Hajarul Asqallani a cikin littafinsa mai suna الدرر الكامنة (Aldurul Kaminah), ya bada kissar Karen da ya kashe wani banasare da ya zagi Annabi SAW kamar haka:-

An yi wani zamani wanda nasara suka yi ta yada addinin kiristanci a cikin Kabilun Mogol, wata rana aka shirya babban taro na nasarantar da wasu sarakunan Mogol musulmai, sai wani babban malamin nasara ya kama zagin Annabi SAW, a wurin akwai wani kare da aka daure a wurin, yana fara zagin Annabi SAW sai Karen ya zabura ya afka mishi da cizo da yakushi, da kyar aka kwace shi a hannun karen, sai wasu mutane a wurin suka ce, saboda zagin da yayiwa Annabi SAW ne kare ya cije shi. Sai wannan banasaren yace a’a ba haka bane, shi dai wannan Karen yana da jin Kansa ne, nunin da nake da hannuna yake ganin kamar zan buge shi ne, sai ya cigaba da zagin Annabi SAW, Karen nan ya kara fusata ya tsinka igiyan da aka daure shi da shi, yayi tsalle ya kama wuyan malamin nasaran nan mai zagin Annabi har sai da ya fizge mkogaronsa nan take ya mutu, ance nan take mutane dubu 40 daga cikin kabilar Mugol suka musulunta…

(Aldurul Kamina : Juzu’i na 03 shafi na 202)

Fassara : Rayyahi Sani Khalifa
(Zawiyyar Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria)

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button