Politics Musics

Ta faru Ta Kare : An Rerawa Mai Wakar Barayi Waka shima Yau An rera masa wato Rarara

Advertisment

Ana zargin fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, da cinye wasu makudan kudade da yawan su ya kai miliyan N100m da aka bawa wasu mawakan arewa.

Rahotanni sun bayyana cewar kungiyar gwamnonin arewa ce ta bawa mawakan kudin saboda irin gudunmawar da suka bayar a yakin neman zaben Buhari a shekara 2015.

Wani ma’abocin amfani da dandalin sada zumunta na Facebook, Ibrahim Sanyi-Sanyi, ne ya fara kwarmata maganar bacewar kudin da aka bawa mawakan arewa ta hannun Rarara, amma kuma kudin suka yi batan dabo, kamar yadda shugaban su Haruna Aliyu Ningi ya tabbatar a wata hira day a yi da manema labarai.

Saidai mawaki Rarara y ace zai kira taron manema labarai domin mayar da raddi a kan wanna batu.

Ana cikin wannan harkalla ne sai ga shi wata waka da aka rera dangane da batun cinye kudin da Rarara ya yi ta fito a ranar 2 ga watan Yuni da muke ciki.
Ga kadan daga cikin baitukan wakan kamar yadda shafin mujallarmu ta yanar gizo ta wallafa a shafin ta;

Rarara Ya cinye Milyan Dari Yaje Kahutu Ya Gina Filin Kwallo , Efcc Ga Barawo Ku Kamo shi , Kuyi Ihu Bararwo, Ku tare Ku tare Bera Ya Cinye Milyan Dari, Ku tare Ku tare Kafin Ya Baiwa Mata, Kudinmu bamu Yafe Maka Ba Kolo Allah Ya Isa, Kolo Allah Ya Isa…”

Ku kasance da hausaloaded.com domin zamu kawo muku wannan Waka nan ba dadewa ba. 

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button