Farashin buhun siminti zai iya kaiwa N9,000 a Nijeriya


A kwanakin baya mun kawo muku rahoto akan irin shirin da mai kamfanin BUA siminti wanda yayiwa mutane albishir cewa zai saukar da farashin siminti, amma sai dai kash yanzu kuma munci karo da wani labari marar daɗin ji wanda jaridar dclhausa na wallafa irin yadda farashi zaiyi tashin gwabron zabe inda sai ninka kudinsa kamar yadda sanarwan na fito.
“Kungiyar masu harhada siminti ta Nijeriya ta ja kunnen cewa muddin gwamnatin tarayya ba ta tsahirta shirinta na amfani da tsarin zuba kankare a kan titunan da ake ginawa ba, to farashin siminti zai iya kai wa Naira 9,000 a kasar.
A halin da ake ciki dai, ana sayar da jikkar simintin mai nauyin kilogram 59 kan kudi N5,000 ko fiye a wasu wuraren ,jaridar Dclhausa na ruwaito.
Kazalika, kungiyar ta ja hankalin cewa akwai bukatar gwamnati ta sa baki wajen yawan tashin farashin da simintin ke yi a ‘yan kwanakin nan ta hanyar kai dauki a masana’antar sarrafa simintin.
Kungiyar a cikin wata sanarwa daga Shugabanta Prince David Iweta da Sakatare Reagan Ifomba, ta yaba wa ma’aikatar aikace-aikace ta tarayya da take kokarin yin amfani da simintin a wajen gine-ginen hanyoyi, sai dai ta ja kunnen cewa yawan amfani da simintin zai sa a rika nemansa a kai a kai da kuma hakan zai sa ya yi tsada a kasuwa.”
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





