Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari da angonta Muhammad Turad sun samu ‘karuwar da namiji
An kuma tattaro cewa daga uwar har dan suna nan cikin koshin lafiya. Hakazalika shafin Instagram mai suna mr_mrs_arewa ya nakalto cewa Muhammad Turad ya sanar da labarin samun karuwar tasu a shafinsa, inda ya bayyana cewa sun sanya wa yaron suna Muhammad Zayd kamar yadda legit na ruwaito
Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hanan tare da mijinta Muhammad Turad Sha’aban, sun samu karuwar da namiji a kasar Turkiyya. Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa an haifin dan ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, Solacebase ta rahoto.
Turad ya rubuta a shafin nasa:
“Allah ya azurta ni da matata da haihuwar da namiji! Alhamdulillah. “Mun saka masa suna Muhammad Zayd (Hibbu Rasulallah).“
AdvertismentView this post on Instagram
Idan za ku tuna, Hanan ta auri sahibin nata ne a watan Satumban 2020, a wani gagarumin shagali da aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.