Abin a yaba : Matashiya engr falmata Usman mai gyaran waya salula tana samun dubu talatin a duk rana
Matashiyar mai shekaru 27 mai suna Falmata Usman ‘yar asalin karamar hukumar Mafa, jihar Borno ta bayyana yadda ta fara sana’ar gyaran waya domin cin gashin kanta.
Falmata mace ce mai kamar maza, domin ta kutsa cikin sana’ar da aka san maza ne da shi ta yi zarra a ciki.
Falmata ta ce ta samu horon gyarar waya yayin da suke zama a sansanin ‘yan gudun hijira inda wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna ‘Plan International’ ta zo sansanin su domin horas da mata sana’ar gyaran waya.
Daily trust tayi fira da engr ta ce ƙungiyar baya ga horas da matan da suka yi ta samar da kayan aiki ga wadanda ta horas domin ƙarfafa guiwowin matan su zage wurin koyan sana’a don cin gashin kan su.
A bayanin da ta yi Falmata ta ce takan samu naira 30,000 a rana a dalilin wannan sana’a da ta fara yi sannan zuwa yanzu ta horas da mata sana’ar.
“Na gamu da nuna wariya da bambanci a kasuwa, da ya ke maza ne aka sani da irin wannan aiki, idan aka ganni a cikin kasuwa sai aga abin ya yi wani bambarankwai.”
“Daga baya sai kuma mutane suka fara kawo min ‘ya’yansu mata, da ƙannen su mata, in koya musu aikin. Kuma a dalilin haka na taimaka wa iyaye na da sauran ‘yan uwana.” Inji ta
Falmata ta ce zuwa yanzu mata 10 ne ke koyan sana’ar a ƙarkashinta.