Labarai

Hukuncin zaben kano : Sharhin Audu bulama bukarti akan hukuncin, dai-dai da Kuskure a cikin bidiyo

Barrister Audu bulama bukarti sunyi sharhi tare da tattaunawa akan hukuncin kotu da tayi akan zaben gwamna jihar kano da ke arewacin najeriya shirin fashin baki na wannan makon ya samu sababbin baki bashir Yusuf Muhammad wanda yana daga ccikin tawagar lauyoyin NNPP, inda shi kuma abdurrazaq A ahmad Esq yana daga cikin tawagar lauyoyin APC.

A cikin wannan tatatauwa anyi tsokaci ne sosai akan wannan abubuwan da ankayi akan hukuncin zaben, lauyoyin ukku duk sunyi Allah wadai akan kalaman alkali anya akan cewa masu jajayen hula yan ta’addan ne da kuma yan bindiga kowan su bai nuna amince da wannan kalma.

Hukuncin zaben kano : Sharhin Audu bulama bukarti akan hukuncin, dai-dai da Kuskure a cikin bidiyo
Hukuncin zaben kano : Sharhin Audu bulama bukarti akan hukuncin, dai-dai da Kuskure a cikin bidiyo

Ga sharhin da Audu bulama bukarti da yayi akan fahimtarsa akan abinda ya faru da abinda zai iya faru a kotu ta gaba idan anyi abu na gaskiya da bin doka.

“Ayyana zabe cewa bai kamala “inconclusive” dai dai ne iya fahimta ta da sanin da nayi Wannan yayi daidai akan Abba Kabir Yusuf ya bada tazarar dubu dari da ashirin da yan canji wanda akwai guri dubu dari biyu da wani abu da ba’a yi zabe ba, idan har anka kamala zabe ratar da anka bada bai kai ko bai fi yawan gurin da ba’a yi zabe, to sai an sake yin wannan zaben.

Kuma wannan ba ra’ayi bane da na dauke shi bayan anyi hukunci a’a, domin washe garin zabe barrister Abba hikima ya kirawo ni yake gayamin munka tattauna akan ga abinda ya faru tun a lokacin nace masa a fahimta akan abinda na sani wannan zabe bai kamala ba “inconclusive”.

Kuma a bayan mako da munka yi shirin fashin baki nace indai anje kotu da wuya ba’a sanya zaben bai kamala ba “inconclusive” .

A Gaɓa ta biyu ayyana Gawuna matsayin gwamna ina ganin akwai kuskure a nan..

“Saboda dalili na farko : idan kotu ta yarda gurare dubu dari biyu da wani abu da anka kashe ko ba’ayi ba, yakamata a sake zabe, kuma Abba ya da samu ratar kuri’a duri dari da ashirin da yan canji ratarsa bata kai yawan kuri’u dubu dari biyu da yan canji, to gawuna da ya samu ratar kuri’a dubu talatin da shidda da yan canji, bayan lissafin kotu to shima ratar taba kai yawan kuri’un duru dari biyu da yan canja da ba’ayi zabe ba .

A fahimta ta, da kotu cewa tayi shi gawuna yana kan gaba yana da kuri’a dubu talatin da shida da wani abu bai kai yawan kuri’un da anka kashe tunda an cire kuri’un abba kabir duri dari da sittin da ukku da wani abu, to sai a koma a sake zabe sai hada da wannan duk wanda yafi yawan kuri’u shi ya chi.

A fahimta ta ta biyu: kuri’u dubu dari da sittin da biyar da kotu tace ta kashe baya cikin da’awar APC tunda basu saka shi akwati bayan akwati “ward by ward” ba guda kaza a wuri kaza lalatattu bane, basu sanya “bleadings” dinsu a da’awar su ba, to ita kotu bata kallon shedda sai anyi da’awa daidai tunda ba’a yi da’awa wannan kuri’a dubu dari da sittin da biyar , ba dai-dai bane ita alkaliyar ta zauna a ofishinta da “calculator” dinta ta cire su tace haramtattu ne, tunda ba’a yi da’awa su dalla dalla ba a cikin takardar su Apc ba, a fahimta ta kenan – inji bulama.

Bulama ya cigaba da kawo nashi hujjojin da suna da yawa ga bidiyon nan ku saurara domin jin hujjarsa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button