Labarai

Yan bindiga sun saki bidiyon daliban Kaduna 39 da suka sace, sun bukaci N500m, sun bada lambar kiransu

Advertisment

Yan bindigan da suka sace daliban makarantar FCFM Afaka a jihar Kaduna sun bukaci N500m daga wajen gwamnatin jihar domin fansan dalibai 39 – Mata 23 da Maza 16.
Daily Trust ta rahoto cewa akalla iyayen uku cikin daliban sun tabbatar da cewa yan bindigan sun tuntubesu kuma sun bukaci N500m kafin su sakesu.
Hakazalika ya bindigan sun sakin bidiyoyi uku na daliban da suka sace cikin daji.
Har yanzu gwamnatin jihar Kaduna ba tayi jawabi kan bidiyoyin ba kuma kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ki amsa wayansa yayinda ake tuntubesa.
Amma, gwamnan Nasir El-Rufa’i a hirar da yayi a tashar Channels ya ce bai zai yi sulhu da yan bindigan ba kuma ba zai biya kudin fansa ba.
Yan bindigan sun yi amfani da shafukan Facebook na daliban wajen sakin bidiyon.
A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda yan bindiga suka zagayesu sanye da kayan Sojoji suna zanesu.
A cikin bidiyon da aka saki misalin karfe 12:00 na ranar Asabar ta manhajar Facebook na Tasha Sandra, ana iya ganin daliban cikin daji tare da yan bindigan sun dukansu.
Tasha Sandra tace: “Wannan ba bidiyon bogi bane. Ku taimakemu ku biya kudin da suke bukata kuma kada kuyi kokarin turo Sojoji ceto mu saboda zasu kashemu.”
“Ina kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha su kawo kudin fansa N500 million. Ga lamba daya tilo da za’a iya samunsu 09023404650.”
Daya daga cikin daliban yace: “Suna na Abubakar Yakubu. Dalibin kwalejin gwamnatin tarayya na ilmin gandun daji Kaduna. Ina kira ga gwamnan jihar Kaduna, gwamnatin jihar Kaduna da gwamnatin tarayya.”
Ga bidiyon nan kasa ku kalla.
https://youtu.be/zrIAUSznioc
Wannan shine link din Tasha sandra da ta dora bidiyo yau
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=10158184962301733&id=645381732

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button