sabon hoton mufti menk sanye da babbar riga ya janyo cece kuce


Wani sabon hoton shahararren Malamin nan na addinin Musulunci na duniya, Mufti Isma’il Menk, ya sanya mutane tofa albarkacin bakunansu a shafukan soshiyal midiya.
A cikin hoton wanda shafin Instagram na northern_hibiscuss ta wallafa, an gano Shehin Malamin sanye da dinkin babbar riga wacce ta ji aiki da kuma hula zanna bukar.
@muftimenkofficial gaskiya da gangan yayi wannan hoton.
Da jallabiyar sa ma matan arewa sun mace bare yaci baban riga da zanna bukar?
Kun tuna kwanaki wata har an saka rana tayi cancelling ita se mufti? Har yazo page din mu ya bata hakuri?
Lol yanzu za ku fara ganin shi a gaban hausa novel a kasuwar rimi.
Novelists would write
“Fari, ga kasumba ga iya kira’a mahaddacin kur’ani asali jikan larabawa ne. Ga iya lafazi hanci kamar biro hakwara kamar madara.”
View this post on Instagram
Tuni dai mabiya shafin musamman mata suka fito domin tofa albarkacin bakunansu
Legit ta zakulo wasu daga cikin sharhin a kasa:
sadia_nas ta yi martani:
“Na yi crushing kan mutumin nan, har dai na hakura da yanzu shi ne Uban ‘ya’ya na “
Rushewar benen Ikoyi: Yawan mamata ya kai 20, ana kokarin ceto wasu a cikin ginin
elegant_glitz_sparkle ta rubuta:
“Yau kam lower your gaze dinnan,,da mata akeyi”
zinariyah_spa ta ce:
“Masha Allah. Abincin wani gubar wani. Duk namiji mai gashi a fuska haka ba dani ba.”
spytro_kids ta ce:
“Mazan arewa sun bar dakin “
teemamzakari ta yi maryani:
“Nikuwa wlh abunda bantabayi ba kenan waishi crushing haka kawai.
k_t_z_clothing_08066401709 ta ce:
“Wannan itache the most expensive babbar riga A kasar hausa sunanta BULLA “
batoul_emporium:
” ya hadu no be lie. Astaghfirullah”
Mufti Menk ya gabatar da Lakca a taron murnar cikar Sarkin Musulmi shekaru 15 kan mulki.
hajara_haidar:
“Ayi mai magana in kishiyar tawa zata bari nashi go biyayya sama da kasa wlh danaga yayi posting naso nayi comment nayi shiru yanzu ma danayi an sosamin gun da yakemin kai kayi ne”
Sady_health
“Gaskiya haramun ne ya dinga sa ka irin wannan hoton, Saboda Allah ya haramta zalunci, yanxu wadanda ya sacewa zuciya suna da yawa”
A wani labarin, Shahrarren Malamin addinin Musulunci a duniya, Mufti Isma’il Menk, ya gabatar da muhadara a taron cikar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Shekara 15 akan Karagar Mulki.
A jawabin da Masarautar ta saki a shafinta, Mufti Menk ya yi jawabi ne kan muhimmancin zaman lafiya.
Wannan taro ya gudana ne a dakin taron Conference Hall dake Kasarawa Sokoto.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





