Labarai

Hukuncin zaben kano yasa Miji ya saki matarsa

A jiya ne dai kotun sauraren kara ta tabbatar da cewa Nasiru Yusuf gawuna shine wanda ya lashe zaben jihar kano akan aringizon kuri’a da anka cire shine ya baiwa gawuna nasara a kotun.

Shine matar ta turawa Nancy journal wannan sakon wani shafin sada zumunta da ke Instagram inda tayi bayyani dalla dalla aka abinda ya faru ita da mijinta har ya sake ta.

Hukuncin zaben kano yasa Miji ya saki matarsa
Hukuncin zaben kano yasa Miji ya saki matarsa

Mijina ya sakeni dazu da yamma akan musun zabe tsakanina sa da”

“Hello Nancy mijina ya sakeni dazu da yamma bayan fadar sakamakon zabe na cewa gawuna yaci, shi kuma dan gawuna ne kuma dan kasuwa , saboda yawancin yan kasuwa sunfi yin gawuna.

Nan fah mukah fara musu dashi akan wallahi Allah hukuncin da aka yanke karya ne,magudi ankayi ba gaskiya ba, na ringa zagin Apc saboda da rashin gaskiyar ankayiwa dan Jam’iyar NNPP , ni kuma jam’iyar tace, na fa fada kara zafi har yace tunda bazan bi ra’ayinshi ba da jam’iyyarshi naje gida ya sake ni, yanzu haka gani a gidanmu.

Gaskiya ce kuma bazan daina fadamai ba, nidai fatana Allah ya zaunar mana sa kasarmu da jaharmu lafiya, Allah ya zaba abin dayafi alkhairi a tare da mu Amin ya rabbi” – inji matar da mijinta ya sake ta.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan wannan wannan sako na wannan matar mun tattaro muku kadan daga ciki.

@dr_haswann cewa yake : Kina wane gida.?
Gidanku ko gidansu Abba gida gida ko gidansu kwankwaso abinda nake na gane.

Taya zakiyi garmada marar tushe da ma’ana da mijinki akan abinda baida muhimmanci .

@zainab_ruma cewa take :

Na daya dai mijinki daman so yake ya sake ki, tunda su sukaci ai kamata yayi ace zuciyar shi bata wuya, na biyu gardama indai bata shiga aljanna bace idan kaji tayi zafi especially da na gaba da kai ai shiru ake, ko da friend kike gardama kika ji tayi zafi haka tunda har ba aljanna ake rabawa ba ai sai kiyi shiru, shiyasa gardama bata da kyau a musulunci balle ma irin wannan marar issassar fa’ida, shawara ki tsaya gida kiyi idda kafin nan ya sauko ki bashi hakuri dan abun kunya ne kije gida kice ga dalilin saki.

@ahmerd_jr cewa yake :

Yau ga ranar Jahilci a kowane bangare
Kinbi Abba shi kuma yabi Uban Abba, kinga ko anan yana samanki.

@cele_cakes_nd_snacks cewa yake :

Ga maganar Sheikh Guruntum ya fito. Wannan laifin, dama wanda yayi ne yasa abin yayi zafi. Ba laifin bane jigo, a’a, wanda yayi. Kila da abokin shi ne, lafiya lau, kila ma gobe har a gaisa. Amma matar shi ce tayi. Kila dama dai akwai wata makarkashiya, aka fa ke da musu. Sannu poster. Shi musu bashi da wani amfani fa. In yace abu black ne, ki bar mishi a black din koda nan gaba an daidaita. Allah ya kara kiyayewa.

@huzaifa sabo cewa yake :

Ita wannan mai rubutun ya kamata ta gane tun am March 18 da akayi zabe, inconclusive ne constitutionally, amma sbd lokacin gwamnatin tarayya bata tare damu tasa aka basu zabe, bayan anje kotu aka Gano akwai kuri ‘un bogi kuma aka kai shedar wadannan kuri’u, da Aka ciresu sai akaga tun asali gawuna ne yaci da kuri’a 30k+.
Yanzu gaskiya tayi halinta amma anace muku kwacewa akayi……..
Murdiya kukayi allh ya tona asirinku, kuma ke banda abinki mijinki yana dan Kasuwa May be an taba kasuwancinsa amma kizo kina musu dashi,,,,, to wace irin tunani ne dake, ko kina ganin abba zai kawo miki abinci har gida ne.

@authman3 cewa yake :

Sai ki Shiga list auren zawarawa kafin abba ya sauka.

@kaltex collection cewa suke;

Amma dai baki da wayo, har yaushe zaki bari har kiyi musu ma akan siyasa, da mijinki ma for that matter, gara ki koma ki gyara gidanki hajiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button