ALLAHU AKBAR Labari Mai Dadi Gareku ‘Yan Uwa Musulmi Akan Mubarak Bala Wanda Yayi Ɓatanci Ga Manzon Allah (S.A.W)
Jaridar Opinion Nigeria ta tabbatar da labarin cewa dakarun ‘yan sanda sun samu nasaran kama wannan kafuri Mubarak Bala shugaban kungiyar “Humanist Association of Nigeria”, an kama kafurin a garin Kaduna dazu da yamma
Wasu jami’an ‘yan sanda ne masu binciken sirri guda biyu a cikin farin kaya suka kama kafurin a gidansa bayan anyi tracking maboyarsa a garin Kaduna, an wuce dashi ofishin ‘yan sanda dake Gbabasawa a nan Kaduna
Bayanan da jaridar Opinion Nigeria ta tattara ya nuna cewa, kama Mubarak Bala yana da nasaba da yin batanci ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW)
Akwai wasu Lauyoyi musulmai masu kishi daga jihar Kano wadanda suka rubuta takardan koke suka aikatawa gwamnatin jihar Kano domin ta gurfanar da Mubarak Bala a gaban kuliya bisa batancin da ya yiwa Annabi Muhammad (SAW) a shafinsa na Facebook, wani lauya mai suna S.S Umar shine ya sanya hannu a takardan koken
Sai dai tuni mabiya kungiyar kafurai ta “Humanist Association of Nigeria” suka nuna takaici da bacin rai bisa kama shugabansu kafuri Mubarak Bala, sunce yanzu haka ana kokarin wucewa da shugabansu zuwa ga hukumar ‘yan sanda reshen jihar Kano domin su gudanar da bincike su gurfanar dashi a kotu
Kungiyar ta su Mubarak Bala tace hukuncin batanci wa Annabi Muhammad kisa ne a shari’ar Musulunci, don haka suna kira ga shugaban ‘yan sanda na kasa IGP Muhammad Abubakar Adamu da gwamnatin jihar Kaduna da su tabbata an saki shugabansu Mubarak Bala.
Wanda ya sa hannu a wannan koken shine
Leo Igwe Ph.D
Chair, Board of Trustees, Humanist Association of Nigeria
Kamar yadda jaridar Opinion Nigeria ta tabbatar da bayanan
Hakika ni Datti Assalafiy nayi farin ciki marar misaltuwa da kama wannan kafurin, jama’a kunga alkalamin rubutun mu yayi matukar tasiri, wani abinda na boye ban fada muku ba, a lokacin da muke neman sahihan nambobin wayar wannan kafuri ko na abokansa, da muka samu aka tura sashin binciken sirri na ‘yan sanda reshen jihar Kano, cewa sukayi an jima ana neman Mubarak Bala amma ya buya
Don girman Allah duk wanda yake da iko a jihar Kano ya tabbata an zartarwa wannan kafuri hukunci, duk abinda zai faru sai dai ya faru, don an kawar da wannan shi kadai ba abinda zai biyo baya face alheri Insha Allah
Yaa Allah AL-HAYYU AL-QAYYUM Ka tabbatar da halaka akan wannan kafuri