Labarai

Da Mijina Ya Yi Min Kishiya, Gwamma Ya Rika Kwanciya Da ‘Ya`yanmu

Wannan wani shiri ne da gidan Jaridar Leadership hausa ta ke kawowa wanda a wannan lokaci ta kawo wani labari mai ban mamaki da al’ajabi wanda duk wanda yaji sai yayi matukar mamaki da shiga wani tunani irin wannan ikari na wannan matar.

Kishi kumallon mata. Shafin TASKIRA shafi ne da yake zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, wadanda suka hadar da; Zamantakewar aure, Rayuwar yau da kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu. Sai dai kuma shafin yakan canja akalarsa wani lokacin wajen maida hankali ga karbar sakonnin masu karatu, musamman masu matsalolin da suke bukatar a tattaunawa a kai dan samun mafita da shawarwarin ma’abota shafin.

Tsokacinmu na yau wani babban al’amari ne wanda shafin ya ci karo da shi, wani labari ne me ta da hankalin mai hankali, wanda yake cike da ban mamaki da al’ajabi, wanda aka nemi a sakaya suna. Labarin dai shi ne: Wata mata ce bahaushiya, musulma, me tsananin kishin tsiya, wadda kishin nata ya wuce misali, kishi ne tamkar irin na masu tabin kwakwalwa. Wadda ke da kusanci da matar da har ila yau ita ce ta aiko mana da wannan sakon ta ce;

‘Matar ta yi ikirari a kan cewa; Da Mijinta ya yi mata kishiya gara ya dinga amfani da yaranta mata da Allah ya ba su guda biyar, matar ta ce; a duk ranar da yake da bukata ya gaya mata wacce ya ke bukata za ta kawo masa ita da kanta’. Wa’iyazubillah.

Ko ya za a kira hakan da shi? Wadanne hanyoyi ya kamata mata su bi domin tursasa zukatansu, da bawa kwakwalwarsu damar yin tunani me kyau ko dan gudun fadawa tarkon da-na-sani?

Wace irin shawara zaku baiwa wannan matar da take da wannan mummunan tunani kishi har ya wuce wuri haka.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button