Labarai

A Najeriya ban taba ganin gwamnati wadda ta kawo masifa irin ta Buhari ba- Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana siyasar ubangida da babbar illar mulkin dimokraɗiyya a tsawon shekaru 25 a Najeriya

Attahiru Bafarawa ya shaida wa BBC hakan ne a wata hira da ya yi dangane da cikar mulkin dimokraɗiyya 25 ba tare da katsewa ba.

Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya ƙara da cewa gwamnatin tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ita ce ta fi kowacce muni a shekaru 25 na mulkin dimokraɗiyya musamman ta fuskar rashawa da cin hanci

“Ka ga duk wani wanda zai iya kare Buhari ko gwamnatinsa to za mu haɗu a lahira domin Allah shi ne babban alƙali amma bala’in da Buhari ya kawo ƙasar nan dangane da dimokraɗiyya na cin hanci ban taɓa ganin gwamnati wadda ta kawo mana masifa a rayuwata ba irin ta Buhari…” In ji Bafarawa.

To sai dai ya yaba wa gwamnatin shugaba Obasanjo wadda ya ce ta ba su dama irin wadda ba a taɓa bai wa gwamnoni ba a tsawon mulkin dimokraɗiyyar, inda ya ce an sakar musu mara su yi abin da suke so a jihohinsu.

Saurari firar a nan bidiyo.

Wani ƙalubalen da tsohon gwamnan ya ce shi ma ya yi wa dimokraɗiyya dabaibayi, shi ne yadda aka talauta ‘yan Najeriya amma idan lokacin zaɓe ya yi sai a fito musu da kuɗi.

“Hakan ya janyo jama’a sun zama mayunwata.” In ji Bafarawa.

Ki 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button