2018 : Bayanai Da Suka Shafi Lakurawa masu ikirarin jihadi
A yanzu labarin Lakurawa ya isa kusan ga kowa, Gwamnatin Nigeria ta tabbatar da bayyanarsu, har ma tayi alwashin zata gama da su a dan kankanin lokaci kamar yadda Shugaban Sojoji ya bayyana
Lakurawa sun fara bayyana a Sokoto tun a shekarar 2018, amma an samu nasaran koransu a farkon shekarar 2019, sun sake dawowa suka kashe Hakimin garin Balle dake karkashin karamar hukumar Gudu jihar Sokoto, suka kona Ofishin ‘yan sanda sannan suka kashe DPO a lokacin
Bayan anyi wannan rigimar dasu tun lokacin basu kara dawowa ba sai a watan August cikin wannan shekara na 2024, fitaccen maabuci amfani da kafar sada zumu Datti assalafy ne ya wallafa.
A yanzu haka Lakurawa suna zaune a babban sansaninsu dake cikin tsibirin dajin Tsauna dake kamaramar hukumar Illela jihar Sokoto, kusan zan iya cewa sun kwace iko da kananan hukumomin Illela, Gudu da Tangaza duk a jihar Sokoto, su kan je hara-hare a Binji da Silame
Bayan haka Lakurawa a yanzu haka sun kori duk barayin daji masu garkuwa da mutane a wadancan kananan hukumomi da suke da iko, kuma sun dorawa al’umma harajin dole na amfanin gona, sannan suna fitar da zakkar dabbobi
Basu tsaya a nan ba, Lakurawa sun hana ko wani irin biki, haduwar Maza da Mata, shan sigari da wiwi, zuwan mata Gona da kuma aikin vigilante, sun tilasta tsayar da gemu da dage wando ga maza, sun tilasta mata sanya hijabi a dukkan kananan hukumomi da sauran kauyukan da suka kwace iko
Lakurawa suna yakar jami’an tsaron Gwamnati da na ‘yan sa kai da barayin daji masu garkuwa da mutane, sannan suna shiga Masallatai suyi wa’azi irin na masu neman kafa Gwamnatin Mu$u|unci da bakin bindiga
Bincikena ya tabbatar min da cewa akwai har da lambar waya da suka bawa mutanen garuruwan da suka musu mubayi’ah, sukace su kira idan bandits sun shigo zasu kawo musu dauki
Wannan shine bayanan sirri a takaice da na hada a kan wadannan mutane Lakurawa.
Ga wasu abu guda uku da ya kamata ayi nazari a kansu don a fahimci barazanan da za’a fuskanta
(1) Wadannan Lakurawa sun zo wa mutane da salon yaudara irin na addini suna cusa wa mutane akida na ta’addanci, anan sai wanda Allah Ya kubutar, domin ilimin tsaro a bangaren sulhu da magance ayyukan ta’addanci ya tabbatar da cewa mutanen da suke ta’addanci saboda akida na addini sun fi wahalar magancewa fiye da wadanda suke ta’addanci saboda daukar fansa, neman ‘yanci ko neman kudi ko zalunci
(2) Kun ga yadda Lakurawa suke bada kudade masu yawa ga duk wanda ya amince zai shiga cikinsu?, idan matashi ne suna daura masa aure da sabuwar budurwa, to ta irin wannan salon zasu ja matasa da yawa sosai, kwatancin yadda B0k0 Ha@ram suka yi, matashi yana zaune ba aiki ba sana’a kuma yana son aure abune mai sauki a ja ra’ayinsa idan zai samu biyan bukata
(3) Mutanen kauyuka suna ta kuka cewa Gwamnati ta gagara karesu daga cutarwan bandits, sai ga wasu masu masu ikrarin jihadi sun zo sun share musu hawaye, suna yakar bandits din, kun ga ai dole su musu mubayi’ah, don haka wannan babban kalubale ne wa Gwamnatin tarayyar Nigeria
Me ya kamata Gwamnati tayi don ta dakile yaduwar wadannan mutane?
Su waye za’a zarga da daukar nauyin su?
Idan na ga babu matsala akwai bukatar bayyanawa zan yi a rubutu na gaba Insha Allah
Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya mana maganin wadannan mutane da masu taimakonsu ta kowace irin hanya