Labarai

Kalaman Gwamna El-rufai Sun Jawo Za A Yi Addu’a A Jihar Katsina Kan Rasuwar Yar’adua

A yau Juma’a ne aka shirya gabatar da gagarumar addu’a bayan sallar Juma’a a kowane masallacin Juma’a da ke fadin jihar Katsina kan zargin rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa ‘Yar’Adua.

Ustaz Muhammad Sada na Kungiyar Matasa Musulmi, reshen jihar Katsina wanda ya bayyana wannan kudirin, ya ce,  wannan addu’a za a yi ta ne a duk masallatan Izala da Darika da ke fadin jihar Katsina.

Ya kara da cewa, babban makasudin yin wannan addu’a shine akan kalaman da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya furta game da rasuwar marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Musa ‘Yar Adu’a.

A wani bangaren kuma wata kungiyar mai rajin hadin kan matasan Jihar Katsina ta shirya wata zanga-zanga a kowace ranar Juma’a idan har Gwamnatin Tarayya ba ta dauki wani mataki ba akan kalaman Gwamna El-Rufa’i ba.

Shugaban kungiyar Alhaji Sabi’u Tanko Safana ya ce, mutanen Jihar Katsina har yanzu suna cikin bakin cikin rashin ‘Yar Adua kuma ba su ji dadin kalaman Gwamna El-Rufa’i ba.

“Mun yi tunanin gwamnan Jihar Katsina zai mayar wa takwaransa Gwamna El-Rufa’i raddi amma muka ji shiru.” In ji Shugaban matasan.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button