Mun gaza gano dalilan da suka hana coronavirus tafka barna a Afrika – Bill Gates
Hamshakin attajirin duniya Bill gates yace har yanzu an kasa tattara gamsassun bayanan da za su fayyace dalilan da suka hana annobar coronavirus ko Covid-19 tafka barnar halaka miliyoyin rayuka a nahiyar Afrika, kamar yadda hukumomin lafiya suka yi hasashe a watannin baya.
Bill Gates dake tsokacin cikin sakonsa na karshen shekara, ya bayyana farin ciki bisa kuskuren da yayi a baya, na bayyana fargabar cewa annobar ta coronavirus za ta halaka miliyoyin mutane a kasashe matalauta.
Bayan shafe shekara guda da barkewa, kawo yanzu adadin wadanda cutar ta kashe da kuma wadanda ke kamuwa da ita na kasa matuka, idan aka kwatanta da ta’adin da annobar ke yi a Amurka da nahiyar Turai.
Kamar yadda rfihausa na ruwaito,alkaluman lafiya na baya bayan nan sun nuna cewar, adadin mutanen da cutar Korona ke halakawa a Amurka, ya zarta barnar da take yi a Afrika ta Kudu da kashi 50.
A farkon shekarar 2020 ne dai hamshakin attajirin na duniya Bill gates yayi gargadin cewa Afrika za ta iya zama nahiyar da annobar Korona za ta fi yiwa barna a duniya.
A halin yanzu rayuka sama da miliyan 1 da dubu 750 cutar Korona ta lakume, daga cikin akalla mutane miliyan 79 da suka da ita. A Amurka kadai mutane dubu 330 da 229 suka mutu a dalilin cutar, yayinda nahiyar Afrika ta rasa jumillar mutane dubu 61 da 930, daga cikin miliyan 2 da 625 da 723 da suka kamu.