Labarai

Atiku ya caccaki gwamnatin Tinubu kan karin farashin man fetur

Advertisment

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya caccaki shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan abin da ya kira gazawarsa wajen tafiyar da sha’anin makamashi.

Atiku Abubakar wanda ya yi takara da Tinubu a zaɓen 2023, ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis cewa gwamnatin Tinubu ta lalata al’amura da sunan cire tallafin mai.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya danganta matsalolin da ƴan Najeriya ke fuskanta da irin tsarin gwamnatin Tinubu na “ta ci barkatai” kan yadda take tafiyar da sha’anin makamashi.

Atiku ya kuma bayyana damuwa kan ƙamarin da hauhawar farashi ya yi a ƙasar inda ya ce al’amarin da matuƙar ƙuntata wa ƴan Najeriya.

“Riƙon sakainar kashi da wannan gwamnatin ke yi wa tsarin cire tallafin mai shi ne babban dalilin da ya sa muke cikin yanayin ƙunci da muke ciki a ƙasar nan.

“A yanzu haka, babu wani fata dangane da hauhawar farashin kaya wanda ya karya ƙarfin tattalin arziƙin ƴan Najeriya.

“Abin takaici ma shi ne yadda al’amarin ba ya damun T-pain,” Kamar yadda Atiku ya rubuta.

BBC Hausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button