Labarai

Matsin rayuwa: ‘Ana zaluntarku kun kasa komai, Amaechi ya yi kira ga matasa da su yi zanga-zanga



Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda ƴan Nijeriya su ka zauna suna kallo an jefa su cikin mawuyacin hali na tattalin arziki.

Da ya ke magana a wata hira da gidan talabijin na ABN TV, Amaechi ya yi tambaya kan dalilin da ya sa ‘yan Najeriya ba sa kwarmata halin wuya da su ke ciki, yana mai nuni da hauhawar farashin kayayyaki da kuma rashin iya biyan bukatun yau da kullum kamar man fetur.

Tsohon gwamnan na Rivers ya ce shi kan sa ba zai iya siyan dizal ba.

Amaechi ya ce yana sa ran matasa za su mamaye tituna daban-daban su yi zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa.

Ya ce: “Ina fushi da ’yan kasa. Na sha fadi hakan. Za ka ga gungun mutane suna sace maku kudi suna talauta ku, ba za ku iya siyan mai da komai ba.

“Ya kamata mutane su yi fushi. Kamata ya yi a yi zanga-zanga. Ba ma zanga-zangar adawa da kowa ba sai ga ’yan siyasa. A rika cewa ‘ba za mu zabe kuba” in ji shi.

Daily Nigerian Hausa









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button