Nima a cikin yunwa nake ina bukatar agaji – sanata Rufa’i Hanga
A cikin wata tattaunawa da ankayi da sanata na tsakiya a jihar kano Rufa’i hanga akan zanga zanga.
Sanata Rufa’i Hanga yace wannan bai dace ba domin a duba irin yadda ta maida wasu kasashe irin su Libya gashi nan sai da bayi ake yi da sauran kashe babu zama lafiya.
Muda ake gani ana ce mana barayi to ba mune ɓarayin ba akwai dai barayin domin nima a cikin yunwa nake, ina da bukatar agaji, kaga sanata ne ni a yunwa nake ina bukatar agaji.
Ina fatan shugabanina su ji, ina yunwa ina bukatar agaji.
tabbas ana cikin yunwa kam ana shan wahala ana cikin matsi, akwai yunwa akwai talauci akwai rashin aikin yi.
Amma ni abin da nake gani talakawan nake tausayawa saboda idan ankayi wannan zanga zanga ba’a san inda zata kare ba.
Ga bidiyon nan ku saurari cikakken bayyanin sa.