Labarai

Sarkin Kano Zai Auri Tsohuwar Budurwarsa

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yana shirin angwancewa da tsohuwar sahibarsa wadda ake kira da suna Hajiyayye dake garin Dorayi a Kano.

Sarkin wanda matarsa ɗaya da ƴaƴa hudu zai yi auren bayan tsahon lokaci yana zaune da mace ɗaya.

Jaridar Daily Nigerian tace majiyarta ta bayyana mata cewar tuni shiri yayi nisa don tattaunawa da waliyyan yarinyar don sanya lokacin auren.Sarkin Kano Zai Auri Tsohuwar Budurwarsa
Majiyar tace an sha ɗaga lokacin auren sakamakon an shirya gudanar dashi ba tare da shirya bukukuwa irin na al’ada idan za’a yi aure a gidan sarauta.

“Mai martaba Sarki ya daɗe tare da Hajiyayye tun kafin ya zama Sarki” a cewar majiyar.
An haifi Aminu Ado Bayero a shekarar 1961, kuma shine Sarkir Fulani na 15 da Gwamna Kano Ganduje ya naɗa shi a ranar 9 ga watan Mayu, 2020.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA