Labarai

Kano : Ɓarawo ya sace sadaki a wajen ɗaurin aure

Wani ɓarawo da ba a gan shi ba ya sace kuɗin sadaki a aljihun wakilin ango a wajen wani ɗaurin aure a jihar Kano.

An ce ana zargin ɓarawon ya zare kuɗin ne ana daf da fara ɗaurin auren bayan sallar Juma’a a masallacin Juma’a na unguwar Gadon Kaya dake cikin birnin Kano a yau.

Limamin masallacin, Sheikh Ali Yunus shine ya gano cewa sace kuɗin aka yi yayin da ya tambayi waliyyin ango da ya miko sadakin.

Wata majiya ta shaidawa Nigerian Tracker cewa an daura auren bayan da waliyyin angon ya roki da a yi musu alfarma da su kawo sadakin daga baya, wanda a shari’ar Musulunci a ke kira da ajl.

Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button