Labarai

Farashin abincin Waje, yafi sauki fiye sa na gida a Nijeriya

A yayin da Dala da CFA ke ci gaba da sauka a kasuwa, ana kara samun rahusa a kayakin abincin da ake shigo da su daga waje. Sai dai fa abincin da ake nomawa a kasar kuwa farashin bai sauka har yanzu.

Inda a wannan satin ake sayar da buhun masara N63,000 a kasuwar Mile 12 International Market da ke Lagos,a makonni biyu da suka shude ma haka ake saidawa a Kasuwar.

Ita kuwa Kasuwar Dawanau a jihar Kano kuɗin buhun masarar kara tashi ya yi duk da cewa tashin Dala da ake danganta tashi da tsadar kayan abinci ya sauka, inda a makon nan aka sai da buhun masara kan kudi N62,000, yayin da a makonnin baya aka sayar a N58,000.

A kasuwar Mai’adua jihar Katsina kuwa masarar ta ɗan sauka a makon nan, an dai sai da buhun kan kuɗi N60,000 a wannan makon na watan Shawwal, bayan da a watan Ramadan kuwa aka saida N62,000, an dai samu sauƙin N2,000 kenan kan farashin makonnin da suka wuce.

Hakazalika, masara ta sauka a kasuwar Kashere da ke Karamar Hukumar Akko a jihar Gombe, an sayi buhun masara N56-58,000 a satin nan, sai dai a sati biyu da suka gabata kuwa an sayar a kan kudi N60-65,000.

Ita ma dai kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna Masarar ta fara sauka, an sayi buhun N57,000 a makon da ya gabata, amma a makon nan N55,000 ake sai da buhun.

To bari mu karkare farashin masara da kasuwar Gombi da ke jihar Adamawa, an sayar da buhun Masara N55-56-57,000 a satin nan, yayin da makonnin da suka shude aka sayar a kan kudi N59-60,000 cif cif.

N13,000 a wannan makon, yayin da makon da ya shude ake saidawa N13,300 a Kasuwar.

A kasuwar Mai’adua jihar Katsina ana sayar da taliyar N14,000 daidai a makonnin da suka gabata, sai dai a makon nan, N12,000 ake saidawa, an samu saukin 2000 kenan a wannan makon.
Yayin da a Kasuwar Giwa da ke jihar Kaduna kuwa ake saidawa N14,500, bayan da a makonnin da suka shude ake sayarwa N14,000 a samu karin N500 kenan a makon nan.
To a kasuwar zamani dake jihar Adamawa kuwa, An sai da kwalin taliya N13,200 a makonni biyu da suka gabata,yayinda a wannan makon ake Saidawa N13,000, daidai.
– DCL HAUSA

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button