Labarai

An fara zanga-zangar matsin rayuwa a Neja har matasa sun rufe babban titin Abuja – Kaduna

Advertisment

Fusatattun matasa a ƙaramar hukumar Suleja a jihar Neja sun yi tsinke a kan tituna domin zanga-zangar matsin rayuwa a Nijeriya .

Masu zanga-zangar sun rufe babban titin Abuja zuwa Kaduna a safiyar yau Litinin.

Tuni fusatattun matasan su ka riƙa daga kwakayen masu rubuce-rubuce daban-daban kamar su “mu ba bayi ba ne”, “tura ta kai bango”, “a janye manufofin da ke gallazawa talaka”, “a dawo da tallafin man fetur” da sauran su.

Zanga-zangar ta yi riga malam masallaci domin saura kwano uku a fara zanga-zangar matsin rayuwa da aka shirya a fadin kasar.

Advertisment

Daily Nigerian Hausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button