Labarai

Mutum 550,000 Ne suka yi Nasarar Shiga Tsarin Npower Batch C ~ Minista Sadiya Farouq

Mutane 550,000 Ne Suka Yi Nasarar Shiga Tsarin N-Power, A Rukunin Batch C, Cikin Mutum Miliyan 1.8 Da Suka Yi Jarabawar Neman Shiga Tsarin, Cewar Ministar Jinkai Sadiya Farouq
Ma’aikatar walwala, Kula da Jin kai, da cigaban Jama’a ta ce an zabi akalla mutane 550,000 daga cikin masu neman shiga tsarin N-Power Batch C cikin mutane miliyan daya da dubu dari takwas da suka zo matakin karshe.
Ministar Walwala, kula da Jin kai, da cigaban Jama’a Sadiya Umar-Farouq ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai ranar Talata a Abuja.
Minista Sadiya ta ce a ranar 11 ga watan Maris, ma’aikatar ta bullo da tsarin Gudanar da Harkokin Zuba Jari na Kasa, NASIMS, ga masu neman Batch C.
Ta ce an nemi masu neman shiga tsarin da su sabunta bayanan su na sirri sannan kuma, suyi gwajin kan layi ta hanyar NASIMS Portal.
“A mako na uku na Mayu 2021, sama da‘ yan Nijeriya miliyan daya da dubu dari takwas 1.8M suka samu nasarar sabunta bayanan su kuma suka yi jarabawar Test ta yanar gizo-gizo.
“An ci gaba da tantancewa kuma an gabatar da mutane 550,000 wadanda suka cancanci zabin karshe don daukar 500,000 a duk fadin kasar don yin aiki a matsayin kashin farko na shirin N-Power a rukunin Batch C.
“Wannan shi ne Batch C rukuni na Farko.
Rukuni na biyu na wasu 500,000 kuma daga baya za a yi su ne daidai da umarnin shugaban kasa yadda zai kasancen an cika Miliyan guda 1,000,000 daidai na masu cin gajiyar karkashin rukunin Batch C.
“Ana kiran masu neman da aka tantance cikin 550,000 daban-daban ta hanyar adiresoshin e-mail dinsu da aka bayar kuma ana ba da shawarar farko da su duba sannan kuma nan take su shiga-shiga tashar kai tsaye ta NASIMS sannan su yi Fingerprints.
Daga Comr Abba Sani Pantami

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button