Labarai

Shin Da Gaske Malam Bashir Ahmad sokoto bashi da Lafiya yana neman taimakon kudi wajen Mutane?

Advertisment

Shin Da Gaske Malam Bashir Ahmad sokoto bashi da Lafiya yana neman taimakon kudi wajen Mutane?
Malam Bashir Ahmad Sokoto

A tafsirin Suratu Isra’i wanda Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto yake gabatarwa, yace sati mai zuwa ba za’ayi karatu ba saboda zai je duba lafiyarsa a wani Asibitin Abuja domin duba lafiyarsa.
Shin Da Gaske Malam Bashir Ahmad sokoto bashi da Lafiya yana neman taimakon kudi wajen Mutane?
Wannan bayyanannkarya da wannan mutum ke yadawa

To shine sai aka samu wani mugum mutum barawo kerkechi mai suna ALIYU MUSA BILYA ya fitar da sako a social media yace wai an kwantar da Malam a Abuja, yana cikin mawuyacin hali yana neman taimakon kudi, sai barawon ya saka account number dinsa kamar haka: 312…..7209 domin ya damfari al’ummah, wannan mutum azzalumi ne makaryaci dan damfara, ba’a kwantar da Malam ba, an masa gwaji ne, kuma ya koma Sokoto yana jiran sakamako, sannan lalurar bata kwantar da shi ba
Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto yace a sanar da al’umma cewa wannan mutumi ALIYU MUSA BILYA makaryaci ne kuma mayaudari, ban sanshi ba kuma baida alaka dani takusa da tanesa, don haka kuyi hankali dashi
Dukkan taimakon da muke nema mukanyi anfani ne da Account number mai dauke da sanana: Bashiru Sani Ahmad Account no: 0736223634 Access Bank, ba sunan wani ba, bamu amfani da suna ko Account din kowa bayan nawa wajen neman taimako don gujewa irin haka
Yadda kishiya ta kashe yar kishiyarta saboda zatayi aure
Abinda ke cikin Tiktok fito-na-fito da Allah da tallata aikin Shaidan – Dr Mansur Sokoto
Baya Hallatta Ga Macce Marar Aure ta sanya Hofa ta Fita fira/zance
Abin takaici ma, babu wani taimako dana taba nema hannun al-umma domin zuwa asibiti ko wata lalura tawa takaina ba aikin addini ba, don haka da yardar Allah zamuyi farautar wannan mutum duk inda ya shiga, har sai mun gurfanar dashi gaban shari’ah – MALAM BASHIR AHMAD SANI (Danfili Sokoto)Shin Da Gaske Malam Bashir Ahmad sokoto bashi da Lafiya yana neman taimakon kudi wajen Mutane?
Muna fatan Allah Ya tona asirin Aliyu Musa Bilya domin ya zama darasi ga masu mugun hali irin nasa
Allah muke roko Ya kara wa Malam lafiya da nisan kwana masu albarka Amin

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button