Kannywood

Tsugunne bata kare ba : Nine Na rubutawa Rarara Wakar Fatima mai zogale – Yusuf Dj

Wani matashi mai suna Yusufa DJ yace shine ya rubutawa Rarara wakar Fatima Mai Zogale bisa sharadin za’a biya shi Idan wakar ta sami karbuwa a gun jama’a, Sai dai Dj yace Rarara ya yi murus da maganar biyan nasa

Majiyarmu ta samu wannan labari a cikin wani faifain bidiyo inda ake zantawa da yusuf dj yana mai cewa,:

“Eh gaskiya al’amarin zaku ji daga bakina ni yusuf dj babban mawaki a fadin Najeriya kai bama a Najeriya ba, Afrika gaba daya , gaskiya nayi wakoki da yawa da mutane basu san ninayi su ba, nayi wakar jigida, wakar dijan gala , nazo nayi wakar gidan iko, daga baya nazo nayi wakar duniya makaranta.

Nayi wakoki da dama basu lissafuwa abun da yawa ,amma ban taba fuskantar ƙalubalai ba a waka sai wannan karo, rarara ya samo ni zaiyi wata waka fatima mai zogale sai dai wakar siyasa shi yafi iyawa nace ni ko wane anayi da mu.

Yusuf Dj ya kara da cewa.

“Nace zan rubuta maka wakar fatima mai zogale amma nawa zaka bani sai yace eh ya dau alkawali idan na rubuta masa wakar fatima mai zolage, wakar ta samu suna ta yaɗu akwai wani abu da zai dauka yabani akan ɓata dare na da nayi, har anka wajen da zai dora nace a’a ba haka bane, sai ga shi fatima mai zolage tayi suna Yusuf dj baiyi suna ba da sake .

Kada in baku daɗi gaba daya ku saurara da kanku ku ji ga videon nan.

 

 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button