Labarai

Ba zan damu ba idan wani gwamnan ya zo ya cire ni — Sarkin Kano Sanusi ll

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai damu da yiwuwar wani gwamna ya zo ya cire shi daga sarautar ba.

A 2020 ne tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe rawanin Sanusi daga karagar mulki, biyo bayan rashin jituwa tsakanin su.

Yayin da shi kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya mayar da Sanusi kan kujerarsa, Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarki na 15, ke kalubalantar tsige shi a kotu.

Da ya ke magana da jaridar Saturday Sun, Sanusi ya ce Allah ne kadai ya san tsawon lokacin da zai ci gaba da zama a kan karagar mulki.

Ya ce: “A gare ni, ko yanzu da nake nan, Allah ne kaɗai ya san tsawon lokacin da zan kasance a nan. Zan iya mutuwa gobe. Wani gwamna na iya zuwa gobe ya ce ya cire ni, ba wani abin damuwa ba ne.

“Amma ina farin ciki idan bai taba masarautar ba. Na yi farin ciki da ba zan bar tarihi ba cewa a lokacina ne aka lalata wannan tarihi na tsawon shekaru 1000.

“Don haka, ina godiya ga wannan gwamnati, ina godiya ga Majalisar nan da suka gyara, cewa mun mayar da masarauta yadda take, kuma Insha Allahu idan na mutu ko na bar kujerar nan, magaji na zai gaji aikin da mu ka yi. Ba wai ta kan mu mu ke ba, mu tsarin mu ke so a gyara, ” in ji Sanusi ll.

Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button