Kannywood

Zargin Madigo: Sabon rikici ya barke tsakanin Sadiya Kabala da Jakadiyar Tonon Asiri

Wani sabon rikici ya barke tsakanin jaruma Sadiya Kabala da Jakadiyar Tona Asiri wacce ta yi kaurin suna a shafin sada zumunta na Instagram
– Jakadiyar dai ta sanya wani hoton jaruman biyu Sadiya Kabala da Maryam Yahaya, ta kuma bayyana cewa yadda suka tsaya kusa da juna bai kamata ba domin mutana za su iya zargin su
– Wannan dalilin ne yasa jaruma Sadiya Kabala ta dinga aikawa da Jakadiyar sakon zagi kala-kala
Wata sabuwar rigima ta barke tsakanin jaruma Sadiya Kabala da wata mai tonon asiri a shafin Instagram mai suna Jakadiyar Tona Asiri.

Da farko dai Jakadiya ce ta fara wallafa hoton Sadiya Kabala wanda ta dauka tare da jaruma Maryam Yahaya, sannan sai Jakadiyar ta ce:
“Cabdijam, wato Maryam da kuma Sadiya irin wannan hoto haka, ai sai ku shiga zargi, ga hammatarki duk tayi gumi ya kamata a rika saka hijabi. Allah ya shirya.”

Wannan magana da Jakadiya ta yi ba ta yiwa Sadiya Kabala dadi ba, inda ta shiga bangaren da ake mayar da martani ta dinga surfawa Jakadiyar zagi.
Mutane da yawa suna ganin wannan abu da Jakadiyar ta yi bai kamata ba, tunda hoto dai irin wannan ba yanzu ne aka fara daukar shi ba, bai kamata ta sako maganar madigo a zancenta ba.

Ga kadan abinda tace akan posting din

Ga musanyar bakin da sunkayi kadan daga ciki

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button