Hajjin Bana : Gwamnan kebbi ya baiwa kowane mahajjaci Miliyan 1 cikon kuɗin hajji


Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta amince da bayar da tallafin Naira biliyan 3.34 ga maniyyata 3,344 da ke son zuwa aikin Hajjin bana daga jihar.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa an fitar da kudin ne don kammala biyan karin kuɗin aikin Hajjin bana da ya kai kimanin Naira miliyan 1.9 da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta sanar.
An cimma wannan matsayar ne a wani taron gaggawa na Majalisar Zartaswa da Mataimakin Gwamna, Umar Abubakar Tafida ya jagoranta, a Birnin Kebbi a yau Litinin.
Da ya ke jawabi ga manema labarai kan sakamakon taron, kwamishinan yada labarai da al’adu, Yakubu Ahmad, ya ce an yi hakan ne domin kyautatawar Gwamna Nasir Idris na ganin an tabbatar da kimar addini domin zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
Ya bayyana cewa an fitar da kudin ne da nufin cika wa kowane maniyyaci domin a samu saukin biyan kudin aikin Hajjin na bana gaba daya kafin ranar rufewa.
“A cikin kimanin karin Naira miliyan 2 da NAHCON ta nema a matsayin karin kudin tafiya, gwamnatin Kebbi ta ware Naira miliyan 1 ga kowane mahajjaci yayin da maniyyaci zai cika sauran da kan sa.
“Alhazan da suka riga suka kammala biyan kudin aikin Hajjin, suma za su ji dadin zunzurutun kudi naira miliyan 1 daga gwamnati ta basu ,” in ji kwamishinan
– Daily Nigerian Hausa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





