Labarai
Korona ta kashe fiye da Amurkawa 4000 a rana guda
Amurka ta kafa sabon tarihi game da adadin waɗanda suka mutu sanadiyyar cutar Korona a rana guda, inda mutane fiye da dubu uku da dari tara suka mutu.
Kamar yadda bbchausa na ruwaito,Jami’ar Johns Hopkins wadda ke tattara alƙaluman annobar na Amurka, ita ce ta bayar da adadin mace-macen na sa’o’i ashirin da hudu da suka gabata.
Jihar Carlifornia ta zama jiha ta biyu da ta tabbatar da ɓullar sabon nau’in cutar mai saurin yaduwa, wanda aka fara ganowa a Birtaniya.