Gwaje Gwajen da ya kamata ayi Kafin Daura Aure saboda Gujewa wadannan Matsaloli
Premarital screening A taikace shine gwaje gwaje da aune aune lafiyar ma’aurata kafin a daura aure.shafin Lafiya uwar jiki na ruwaito
Gwaje gwajen lafiya kafin aure na daya daga cikin manyan hanyoyin da ake bi wajen kiyaye aukuwar cutuka, musamman a mata da kananan yara.
Tunda an ce riga kafi ya fi magani, idan aka rungumi wannan hanya ta riga kafi za a iya shawo kan wasu manya manyan cututtuka da mata da yara kan samu wadanda za mu lissafosu a gaba.
Masana kiwon lafiya sun bada shawarar gwaje gwajen lafiya kafin aure domin a tabbatar da cewa ma’auratan lafiyar su kalau sabida gudun kada a cutar da juna daga baya azo a shiga da nasani. Sannan malamai da masana Shariar muslinci da christoci suka bada goyon bayan wannan shawarar.
Wanda yanxu a wassu yankin nan kasa Najeriya kusan wajibi ne sai anyi gwaji kafin Aure.
Amma kash mafiya yawan yankin sun bada karfi ne ga awun HIV kadai, alhalin akoi wanda yafi dacewa ayi kafin ayi na HIV din ma.
Gwaje gwaje da ake kafin daurin aure sun kasu kashi biyu:
1- Masu hana daurin Aure.
2- Wadan da basa hana daurin Aure.
Diyawa daga cikin mu bama bada muhimmanci ga gwajin cututtukan gado na tangardar kwayoyin halittu na gado na DNA wadanda uwa da uba za su iya sa wa dansu.
Abinda mukafi maida hankali shine cututtukan da kwayoyin cuta za su iya sa wa, wadanda miji ko mata za su iya sa wa junansu.
Mesa mafi yawan yan Najeriya kan su, suka sani basa tunawa da wahalar yayan su za su shiga zuwa gaba ??
jerin gwaje gwaje da ya kamata ayi kafin aure:
1- Gwajin cutar sikila (amasorin jini) tana yaɗuwa ne ta hanyar auratayya tsakanin mace da namiji da suke da nau’in na ciwon da a ke kira sikila SS ko AS guda biyu.
Akoi Nauyukan Jinin kamar haka :
– AA ( Lafiya)
– AS ( Akoi Rabin Ciwon)
– SS ( Akoi Ciwon gabaki daya)
1- Mai kwayar jinin AA da mace mai AA akoi aure tsakanin su.
2- Mai kwatar jini AA da AS suma za su iya aure da sanin za’a iya samun mai AS a cikin yaran su.
3- Mai kwayar jinin AA da SS suma za su iya Aure da sanin dukkan yaran da zasu haifa AS ne.
4- Mai kwayar Jini AS da SS Aure tsakanin su akoi matsala gwara a hakura da juna.
5- Mai AS da AS akoi su ma aure tsakanin su akoi matsala a hakura da juna, ayiwa juna fatan Alkhairi.
5- Mai kwatar jini SS da SS babu aure tsakanin su, kawai a hakura da juna.
Insha Allah za mu samu lokoci muyi bayani sosai akan sikila yadda mutane za su gane hatsarin ta.
2- Gwajin cututtuka masu yaduwa ta hanyar jima’i kamar su:
– HIV/AID (cutar kanjamau) Wanda shi wajibi ne, idan ankara da wadannan yanada kyeu sosai.
– Viral Hepatitis
– Gonorrhoea,
– Syphilis.
– Da sauran su.
HIV cuta mai karya garkuwar jiki, idan aka samu daya daga cikin su yana dauke da kwayar cutar yazama wajibi a dakatar da maganar aure.
Hakan baya nufin bazai sakeyin aure a rayuwar sa ba, akoi daman yayi aure mace mai dauke da wannan ciwon suyi rayuwar su.
Haka kuma idan aka bi ka’idodi za su haifi Lafiyayyun yara.
*Shawara*
Kada wani ya yaudare ku da akoi maganin HIV na gargajiya wanda yake warkarwa. Wallahi karya ce da yaudara.
Bama musun ko wacce cuta tana da magani, amma na HIV kam har yanxu duniyar masana basu gano ta ba.
Sai kuma sauran da muka lissafo a kasar sa basa hana aure kai saye, akoi matakai da ake daukawa kafin ayi Auren.
3- Gwajin rukunin Jini (Blood grouping). Diyawa daga cikin mu bamu san amfanin gwajin rukunin jini kafin aure ba.
Gwajin rukunin jini ga masu shirin aure yana da fa’ida, bincike ya nuna cewa macen da ke karkashin dangin jini na Negative idan ta aure wanda ke qarqashin Positive, tana iya fuskantar hatsarin yawan zubewar ciki ko mutuwar dan da ke cikin mahaifa (intrauterine death). Gudanar da irin wannan gwajin na da muhimmanci.
Misali idan mace tana da O- (Onegetive) idan ta auru mai O+ (O positive), sai aga tayi ciki so 6 duke ta barar, ayi ta kulla wa aljanu da sihiri alhalin abin ba haka yake ba.
Wani lokacin kuma idan aka samu bambanci na nau’in jini tsakanin uwar da kuma jariri ko jaririya, ana iya samun matsala wani lokaci yara su zo da ciwon nan da ake kira jondis, wato matsananciyar cutar shawara, wanda idan an haihu za a ga idon yaron ya yi kamar rawaya, sannan kuma jikinsa ma ya sauya launi ya zama rawaya saboda jikinsa yana farfashewa.
Insha Allah zamu samu lokoci muyi bayani akan wannan matsalar sosai yadda mutane zasu fahimta.
Zan takaita anan sabida lokocin da na daukawa kaina ya riga ya wuce.
Ga sauran gwajin kaman haka…
4- Gwaji wassu cututtuka wadanda zasu iya kai ga rabuwar Aure bayan Aure tsakanin miji da mata, kamar cututtukan da ke iya jawo rashin haihuwa, da kuturta, da wasu nau’o’in cutar daji (cancer) masu hatsari, da cutar qoda.
5- Gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa: Likitoci sun bayyana cewa wannan gwaji ne mai matuƙar muhimmanci ga masu niyyar aure domin kaucewa ga matsala.
Haka kuma matslar ƙwaƙwalwar kan zama na gado a lokuta da dama, inda bayan an yi aure abin kan shafi yaran da za a haifa.
6- Sai kuma gwajin juna biyu: Duk da wannan bata daya daga cikin abu mai muhimmancin a wajen turawa, anan Africa musamman Nigeria tana da matukar amfani domin fita daga zargi da cece kuce bayan Aure.