Labarai

Gara na mutu da wannan rayuwar matsi da muke ciki

Tsadar rayuwa na ci gaba da tilastawa ‘yan Najeriya shiga yanayin da ba su taba tunani ba, inda yanzu suke cin abincin da a baya ko dabbobi ba za a bai wa ba,

Jaridar Liberty na ruwaito cewa a yanzu haka, sakamakon tsadar shinkafa, mutane kan sayi wata shinkafa da ake kira ‘Afafata’ wadda ta yi kama da damajin kamfani.

Wata mai jego mai cin shinkafar ta ce gwara ta mutu da ta ci gaba da zama cikin matsin rayuwa.

Gara na mutu da wannan rayuwar matsi da muke ciki
Shinkafa

“Wallahi indai zan samu rahamar Allah na gwammace na mutu da wannan rayuwar da muke ciki. Wannan rayuwa ai mutuwarka ce ta fi sauki.”

Ana dai sayar da kwanon shinkafa nau’in afafata kan naira dubu daya da dari takwas sabanin lafiyayyar shinkafa wadda ta farashinta ya wuce.

Mai jegon ta ce a hakan ma sai dai su sayi gwangwani sannan kuma mutum zai kwashe awa biyu zuwa uku kana tsince datti.

“Kana ci za ka ji daci a bakinka.Wallahi ba na iya cinta.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button