Wasu matasa sunyi garkuwa da iyalan yan bindiga a jihar Zamfara
Abubuwan harka tsaro kullum ci baya take a arewacin Nigeriya musamman arewa maso yamma na yan bindiga inda anka tashi da wani al’amari wanda ya baiwa mutane mamaki sosai irin yadda mutanen gari nayi ciki da iyalan ya bindiga hausawa kance sata gidan barawo rance.
Jaridar yada labarai BBC Hausa ta ruwaito wannan labarin kamar haka
Wani mutumin yankin da abin ya auku, wanda ya gwammace a sakaya sunansa, ya yi karin bayani kan wannan dakasarama:
“Ana ta juyayi sai ga wadannan matan ‘yan bindiga sun zo, sai mutane suka ce ba za su wuce ba kuma ba za su sakesu ba sai an kawo ‘yan uwanmu da aka kama,” in ji shi.
Mazaunin yankin ya ce ‘yan bindigar sun kira matan nasu ta waya inda suka nemisu da su yi kokari a sakesu don suna cikin ‘mawuyacin hali‘.
Matashin ya kuma musanta zargin da ake yi kan cewa mazauna yankin sun dauki doka a hannunsu:
“Wannan an riga an dange mu ne, mun rasa yadda za mu yi da rayuwarmu, ka fita daji ba dadi, ka dawo gida ba dadi, ka yi kwance ba dadi.
Rahotanni sun ce a gona ‘yan bindigan suka sace mutanen na Birnin Magaji, a cewar wani mutumin yankin, wanda shi ma ba ya so a fadi sunansa:
“Su na gona wurin aiki, sai ga wadanan ‘yan bindiga su kusan goma sha,suka zagayesu da bindigogi, to da suka ga sun fi karfinsu sai suka bada hadin kai aka tafi da su “ in ji shi.
Yan bindigar sun sace mutun 7 da farko amma daga bisani daga cikinsu ya dawo gida.
Mutanen da suke garkuwa dasu sun hada da maza 4 da mata 2.
Kallo a yanzu ya koma ne kan yadda wannan ja-in-ja za ta kaya, tsakanin matasa da ’yan bindiga a yankin na Birnin Magaji a jihar Zamfara.