Labarai

Abubuwa 18 da baku sani ba game da Sarauniyar Ingila da ta mutu

Wadannan na daga cikin abubuwan da Sarauniyar England Elizabeth ta 2 da ta mutu yau 8/9/22 bayan sarauta ta kusan shekaru 70, itace kadai ke da su saboda girman matsayinta a duniya:

1. Itace kadai ba ta bukatar license kafin ta tuka mota.

2. Itace kadai ba ta bukatar passport kafin ta shiga kowace kasa a duniya.

3. Itace kadai ke yin murnar ranar haihuwa sau 2 a kowace shekara.

4. Tanada mawakiya ta musamman, wacce ita kadai take yiwa waka. Mawakiyarta kuwa itace Carol Ann Duffy.

5. Tanada ATM dinta ita kadai, na daya daga cikin mafi girman bankunan Birtaniya wato Coutts wanda aka ajiye a gidan sarautar England na Buckingham Palace.

6. Duk agwagin kogin Thames nata ne, don haka babu mai ikon taba ko daya.

7. Duk inda aka ga kifin nan mai suna Dolphin a ko’ina cikin kogunan Birtaniya nata ne, babu mai taba mata su.

8. Babu dokar da aka isa a zartar a Birtaniya ba tareda amincewarta ba.

9. Tanada ikon ta dora ko ta sauke ba tareda shawarar kowa ba.

10. Tanada ikon ta ki biyan haraji, amma kuma tana biya don ganin damarta tun shekarar 1992.

11. Babu mai ikon sa ta ita da iyalanta su yi bayani akan wani abu, ko da a kotu ne. Sunada ikon su boye magana ba tareda an tilastasu sun fada ba.

12. A duk sanda aka samu sabani a kasar, tanada ikon ta iya chanja duk wani ra’ayi na ministocin kasar zuwa ra’ayinta.

13. Dole ministocin kasar su ke tuntubarta, kuma tanada ikon yin fada wa kowa, ko gargadin kowa.

14. Ba Sarauniyar Birtaniya ce kadai ba, itace ma Sarauniyar Australia. Birtaniya ta hada kasashen; England, Scotland, Wales da Northern Ireland.

15. Bayan itace Sarauniyar Birtaniya da Australia har yanzu kuma ita ke da tacewa a wadannan guraren (kasashe da tsibirrai); Antigua & Barbuda, Bahamas, Barbados, Belize, Grenada, Jamaica, New Zealand, Papua New Guinea, Saint Kitts & Nevis, Saint Lucia, Saint Vincent & the Grenadines, Solomon Island da kuma Tuvalu.

16. Itace shugabar Cocin England, babu wani sama da ita a addinance don haka ba za ta taba chanja Coci ba domin itace kan.

17. Babu wanda ya isa ya tuhumeta akan komai, ta fi karfin tuhuma.

18. Tana iya korar gaba dayan masu mulkin kasar Australia ta nada sabon Firayim Minista a duk sanda ta ga dama.

Daga Abu Albani Auwal Ahmad,

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button