Labarai

Masu gidajen burodi sun fara yajin aiki a Nijeriya

Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya (AMBCN) ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukanta daga yau 27 ga watan Fabarairu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa, Mansur Umar, ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan matsaya ce bayan kammala wani taron gaggawa na musamman da ta kira domin matsa wa gwamnati lamba kan ta ɗauki matakin sauƙaƙa kasuwancin masu sarrafa fulawa a ƙasar.

Sanarwar ta ce duk wasu ayyukan haɗawa ko sayar da burodi ya kawo ƙarshe ne a jiya Litinin, 26 ga wata, kuma yajin aikin zai ci gaba har nan da mako ɗaya.

Wannan dai zai ƙara dagula lamurra a ƙasar, daidai lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar – NLC ta kira zanga-zanga ta gama-gari.

Najeriya dai na fama da tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ya kai ga masu kamfanoni ƙara farashin kayan da suke samarwa sanadiyyar hauhuwar farashin kayan da suke amfani da su.

Fulawa na ɗaya daga cikin kayan masarufi da farashinsu ya yi tashin gwauron-zabi tun bayan da ƙasar ta shiga cikin halin tangal-tangal na tattalin arziƙi.

BBC Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button