Abin a yaba : Rarara Ya Tallafawa Mutane 10,000 da kyautar kayan abinchi da na cefane


A cikin wannan tsananin yunwa da tsadar rayuwa wanda ko ina abun sai addu’a shahararren mawakin siyasa a da ake arewacin Nijeriya Dauda Adamu Kahuta rarara yayiwa al’ummar goma ta arziki.
Kwana baya ma shima yayi ta tallafawa yan yankinsa na kahutu rarara, a yau din nan majiyarmu hausaloaded ta samu wannan labari ga mataimaki na musamman a kafafen sada zumunta Rabi’u Garba Gaya ne ya sanar da wannan abun kirki da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
“Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara Ya Tallafawa Mutane Dubu Goma ( 10,000 ) Da Kyautar Kayan Abinchi, Sannan Kuma Ya Ware Naira Miliyan Hamsin ( 50,000.000 ) Ya Bawa Kowannen Su Naira Dubu Biyar – Biyar ( 5,000 ) Domin Suyi Chefane.
Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara Yayi Taron Tallafin Ne a Garin Kahutu Dake Karamar Hukumar Danja a Jahar Katsina.”






![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




