Labarai

Adadin Mutanen Da Aka Kashe Tsakanin Sokoto, Zamfara Da Katsina A Cikin Makonni Biyu Da Suka Gabata Sun Haura 800 ~ Inji Shaikh Yusuf Sambo Rigachikun

Advertisment

…ba na ganin laifin Buhari kan kashe-kashen Arewa saboda ya yi duk abinda ya dace, cewarsa

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Fittacen malamin addinin musulunci dake garin Kaduna mataimakin shugaban Majalisar Malamai na ‘kasa na Kungiyar Izalah, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya bayyana takaicinsa kan yadda ake kashe al’umma a jihohin Katsina, Sokoto Zamfara inda yace alissafin da ya yi a kasa da makonni 2 kadai an kashe sama da mutane 850.

Sheikh Rigachikun ya ce baya ganin laifin shugaban kasa a tabarbarewar tsaro a yankin Arewa, ya ce shugaban kasa ya bawa Arewa dukkan wani mukami a bangaren tsaro sune suka ki yin abunda ya dace

Sheikh Rigachikun ya kara da cewa kisan ran Dan Adam babbban laifi ne a wajen ubangiji. Ya ce ya fi sauki mutum ya rushe dakin ka’aba akan ya kashe ran mumini daya.

Yace Manzon Allah S A W yace “duk wanda ya taimaka aka kashe ran mumini daya koda da rabin kalma ne, to la’antar Allah da fushin Allah da azaba sun tabbata akanshi”

Shehin Malamin ya yi wannan tsokacin ne a yayin da yake gabatar da hudubar Juma’a a massalacin Tunawa da Sheikh Abubakar Gumi dake garin Rigachikun a jahar Kaduna.

A karshe malamin ya yi addu’ar Allah ya kawowa Nijeriya dauki daga miyagun ‘yan ta’adda.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button