Zanga-zanga ta barke a Jami’ar Najeriya har anyi wa VC jina-jina saboda karin kudin makaranta
Ana ci gaba da wata gagarumar zanga-zanga a Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya (wanda aka canza mata suna zuwa Michael Okpara University of Agriculture), Umudike a Jihar Abia.
Rahotanni sun ce an shafe watanni ana zanga-zangar ne sakamakon karin kudin makaranta da aka yi a karshen shekarar da ta gabata.


Mahanga ta ruwaito, lamarin ya ƙazanta ne bayan da hukumar Gudanarwar Jami’ar a karkashin Shugaban Jami’ar, Farfesa Maduebibisi Ofo Iwe, ta fara aiwatar da wani tsari na “Biometric” da ake amfani da zanen yatsun hannu domin tantance daliban da ba su biya kudin makaranta ba a hana su shiga jarrabawa.
Bayanai sun ce a jiya Litinin ne aka fara jarabawar, amma kuma VC da tawagarsa sun fita daga hall zuwa Hall, inda suka riƙa tace daliban da basu biya ba ana fitar dasu,
Sai dai hakan ya fusata daliban har suka dauki doka a hannunsu, inda suka kai wa VC hari, suka kore shi daga makarantar, tare da lalata kayayyakin Jami’ar duk da cewa Jami’an tsaron makarantar sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye amma daƙyar suka iya ceto VC da tawagarsa.
Zanga-zangar ta cigaba da kankama daliban suna rera wakar “No Gree For Anybody”, “we no go gree o”… suna bin VC suna jifan motarsa da duwatsu da sanduna.
Mahanga ta ruwaito kawo yanzu an rufe Jami’ar har sai yadda hali yayi, a gefe ɗaya kuma daliban sun mamaye titin Umuahia-Ikot Ekene, suna kunna wuta da sauransu.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






