lauyan ‘yan shi’ah ya daukaka kara akan hukuncin kisa ga wanda ya zagi manzon allah (saw) ~ Datti Assalafy
Zindiki Aminu Shariff wanda aka yankewa hukuncin kisa bayan kotun Shari’ar Musulunci a Kano ta sameshi da laifin batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), ya samu tallafin ‘daukaka kara daga babban Lauyan ‘yan shi’ah Barista Femi Falana
Babban jakadan sharri Femi Falana wanda yake babban Lauyan ‘yan shi’ah da yake kokarin kubutar da tsageri Zakzaky bisa tuhumar da gwamnatin jihar Kaduna take masa akan laifukan ta’addanci da samar da gwamnati a cikin gwamnatin, ya sake tsayawa wannan kafuri zindiki Aminu Sheriff wanda ya zagi manzon Allah (SAW) aka yanke masa hukuncin kisa
Yanzu haka Femi Falana ya kai karan Gwamnatin Tarayyar Nigeria da gwamnatin jihar Kano, yayi karansu zuwa ga babbar kungiyar kare hakkin bil’adama ta nahiyar Afirka
Datti Assalafy ya cigaba da cewa ,barista Femi Falana a sakon da ya aika; ya nemi kungiyar kare hakkin bil’adama da cewa tayi gaggawan kubutar da Aminu Sheriff saboda wai an take masa hakkinsa na fadin albarkacin baki, inda ake neman zartar masa da hukuncin kisa saboda ya zagi Annabi Muhammad (SAW), wai wannan take hakki ne ba laifi bane inji Femi Falana
Yaa Allah Ka tsine ma wannan Lauya albarka, Allah Ka dusashe tasirinsa, Allah Ka tarwatsa al’amarinsa Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





