Labarai

Sojojin Nijar sun yi luguden wuta kan fararen hula bisa kuskure

Advertisment

Gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan Nijar ta sanar da hallaka fararen hula a ‘yan kasar bisa kuskure a lokacin da dakarun kasar ke kokarin maida martani ta sama da jiragen yaki daga wani harin ta’addanci da wasu mahara suka kai musu a yankin karamar hukumar Gothèye da ke cikin jihar Tillaberi

Jaridar Dclhausa na ruwaito cewa,Ministan tsaron kasar ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar wacce a cikin ta ya ce lamarin ya faru ne a dare Juma’a wayewar Asabar din nan ta 6 ga watan Janairu.

Wannan abu dai ya zamo ruwan dare inda a shekarar da ta gabata ankayiwa masu Maulidi ruwan bama bamai a Nijeriya yau kuma ga abun alam makwabtansu.

Wani labarin: An jana’izar Mutum sama 90 Bayan Harin Jirgin Sojoji Kan Masu Mauludi a Kaduna

Mutanen da suka tsallake rijiya da baya a harin bom da jirin sojin kasan Najeriya ya kai wa masu taron Mauludi sun tabbatar da yin jana’izar sama da mutum 80.

Mazauna kauyan Tudun Biri sun shaida wa Aminiya cewa wasu gawarwakin ma a cikin buhu aka saka su aka yi musu jana’iza.

Wani mazaunin yankin mai suna Liman ya ce sun binne sama da mutum 90, wasu a cikin buhu.

Ya ce akwai wani magidanci da ya rasa matansa biyu da yaya, sai jariri daya da ya tsallake rijiya da baya a harin.

Jaridar aminiya na ruwaito,Wani mazauna yankin kuma, wanda ya samu tsira daga harin, Bello Shehu Gara, ya tabbatar da cewa jirgin sama ne ya jefa masu bon suna tsakiyar bikin Maulidi a garin.

“Muna cikin bikin Maulidi ne sai muka hangi jirgin na shawagi a sama, kafin mu ankara sai kurum ya sako bom wanda ya halaka mutum kusan 57.

“Sai muka hangi wasu na neman taimako, mun kai masu dauki, kurum sai jirgin ya sake sako wani bam din, daga Nan muka gudu,” inji shi

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button